Nigerian news All categories All tags
Korar malamai: Kwamitin mutan Zazzau ya ba El-Rufa'i shawarar yadda zai yi da dakikan malamai

Korar malamai: Kwamitin mutan Zazzau ya ba El-Rufa'i shawarar yadda zai yi da dakikan malamai

Wani kwamitin mutane daga masarautar Zazzau dake tu'ammali da harkokin sadarwa ya shawarci Gwamnan jihar Malam Nasiru El-Rufai da ya ba malaman makarantar da suka fadi jarabawar daliban su 'yan aji hudu damar su kara ilimin su cikin watannin 12 ba wai kora ta gagaf ba.

Wannan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kwamitin ya fita dauke da sa hannun Sakataren su Ibrahim Adamu Zango wanda kuma ya bayyana korar ta malamai 21,780 a gagaf a matsayin wani koma baya da kuma rashin adalci.

Korar malamai: Kwamitin mutan Zazzau ya ba El-Rufa'i shawarar yadda zai yi da dakikan malamai

Korar malamai: Kwamitin mutan Zazzau ya ba El-Rufa'i shawarar yadda zai yi da dakikan malamai

KU KARANTA: Ko da gaske ne kungiyar Izala taci kudin makamai

Legit.ng ta samu cewa a ra'ayin kwamitin, kamata yayi Gwamnan ya ba malaman damar zuwa su koyi karatu su kuma kara ilimi har na shekara daya sannan sai a sake yi masu jarabawar.

Hakanan kuma dai kwamitin ya yabawa gwamnatocin jahohin Kano da Sokoto da suka bi hanya mafi sauki ta koyarwa tare da bayar da horo ga malaman na su a maimakon korar su gaba daya.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel