Nigerian news All categories All tags
Zaben 2019: Gwamnatin Buhari tana barazana ga hadin kan kasa – Inji Atiku

Zaben 2019: Gwamnatin Buhari tana barazana ga hadin kan kasa – Inji Atiku

- Atiku Abubakar ya ce gwamnatin shugaba Buhari tana barazana ga hadin kan Najeriya

- Atiku ya rubuta wasika zuwa ga APC, inda yake sanar da su shawararsa na ficewa daga jam’iyyar

- Atiku ya ce shawar ficewa daga jam'iyyar bai kasance game da shi ba, amma game da makomar kasar Najeriya

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya bayyana gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari a matsayin babban barazana ga hadin kan kasa, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

Legit.ng ya tattara cewa Atiku ya rubuta wasika zuwa ga jam'iyyar APC, inda yake sanar da su shawararsa na ficewa daga jam’iyyar.

Ko da yake ya rubuta wannan wasiƙar ne a ranar 18 ga Oktoba, 2017, amma shugaban jam’iyya mai mulki ta APC a ranar Juma'a ya karyata karbar wannan sanarwa daga tsohon mataimakin shugaban.

Zaben 2019: Gwamnatin Buhari tana barazana ga hadin kan kasa – Inji Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar

A cikin wasikar, Atiku ya ce shawar ficewa daga jam'iyyar bai kasance game da shi ba, amma game da makomar kasar Najeriya.

KU KARANTA: Zaben 2019: Atiku na ci gaba da ganawa tare da shugabannin PDP

"Na gagara fahimtar rashin aikin wannan gwamnatin jam’iyya mai mulki, musamman ma game da yadda al’amuran mutanen mu ke ta barbarewa ta hanyar kabilanci da addini wanda ke barazana ga hadin kanmu fiye da kowane lokaci a cikin 'yan kwanan nan da kuma kalubale da al’ummar kasar ke fuskanta sakamakon durkushewar tattalin arziki", in ji shi.

A cikin wasikar wanda Usman Muazu ya amince da shi, wanda kuma majiyar Legit.ng ta samu, Wazirin Adamawa ya ce; "Ina so in sanar da ku game da shawarar yin murabus daga jam'iyyar APC a wannan rukunin wanda kuma za ta fara daga ranar da wannan wasika ta fito".

"Na yi murabus daga wannan jam’iyyar da muka kafa kuma muka yi tsayin daka tare da 'yan'uwanmu' na siyasa a duk faɗin ƙasar, don mu sanya gwamnati. Ina fata cewa a wancan lokacin gwamnatin APC za ta inganta rayuwar jama'armu da ci gaban Najeriya a matsayin al'umma guda ɗaya. Amma wannan buri ta riga ta rushe”.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel