Nigerian news All categories All tags
Zaben 2019: Atiku na ci gaba da ganawa tare da shugabannin PDP

Zaben 2019: Atiku na ci gaba da ganawa tare da shugabannin PDP

- Tsohon mataimakin shugaban kasa na ci gaba da ganawa tare da shugabannin PDP

- Kawo yanzu Atiku bai bayyana shirin harkokin siyasarsa na gaba ba

- Rahotanni sun nuna cewa Atiku ya sadu da shugabannin PDP daga jihohi 6 da ke yankin arewa maso gabas

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yana ci gaba da ganawa tare da shugabannin babban jam'iyyar adawa ta PDP.

Idan dai baku manta ba Atiku ya yi murabus daga jam’iyyar APC a ranar Juma'a, 24 ga watan Nuwamba.

Kamar yadda Legit.ng ke da labari, har zuwa yanzu Atiku ya yi shiru a kan harkokin siyasarsa na gaba.

Zaben 2019: Atiku na ci gaba da ganawa tare da shugabannin PDP

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar da Sultan na Sakkwato Sa’ad Abubakar III

Rahotanni sun nuna cewa Atiku ya sadu da shugabannin PDP a Adamawa, da kuma shugabannin jam’iyyar daga jihohi 6 da ke yankin arewa maso gabashin kasar.

KU KARANTA: Wata kungiya ta bayyana daliliai 8 da yasa Atiku ba zai taba yin shugabancin Najeriya ba

Abdullahi Prambe, sakataren jam'iyyar PDP, ya ce ganawar ta kasance mai kyau.

"Ganawar mu da shi ya kasance mai ban sha’awa kuma daga yanayinsa zai dawo PDP," inji Prambe.

Prambe ya bayyana cewa dawowar Atiku Abubakar a matsayin babban ci gaba ga PDP.

"Tare da Atiku, jam'iyyar za ta ci gaba da bunkasa kuma daruruwan mutane za su shigo cikin ta sanadiyar Atiku" in ji shi.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel