Nigerian news All categories All tags
Buhari ya biya kudin makaranta miliyan 164.8 na ‘yan matan Chibok 106

Buhari ya biya kudin makaranta miliyan 164.8 na ‘yan matan Chibok 106

- Shugaban kasa ya biya kuɗin dalibai na jami'a na ‘yan matan Chibok 106

- Fadar shugaban kasa ta sanar cewa 'yan matan suna karatu a jami'ar Amurka ta Najeriya wanda ke garin Yola

- Gwamnatin tarayya ta yi alkawarin za a sako sauran ‘yan matan Chibok da ke hannun kungiyar Boko Haram

Shugaban kasar Muhammadu Buhari ya amince da biyan kuɗin dalibai na jami'a na ‘yan matan Chibok 106, fadar shugaban kasa a ranar Lahadi 26 ga watan Nuwamba ta sanar da hakan.

Mataimakin shugaban kasa a kan shafukan yanar gizo Lauretta Onochie ta tabbatar da hakan a shafinta ta Twitter a ranar Lahadi.

Ta ce 'yan matan suna karatu ne a jami'ar Amurka ta Najeriya wanda ke garin Yola, jihar Adamawa, wanda tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya kafa.

Buhari ya biya kudin makaranta miliyan 164.8 na ‘yan matan Chibok 106

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari

Legit.ng ya ruwaito kwanan nan cewa iyayen sauran 'yan makaranta na Chibok sun nuna bakin ciki ga shugaba Buhari game da makomar' ya'yansu wadanda har yanzu suna hannun Boko Haram.

KU KARANTA: Najeriya za ta kashe sama da Biliyan 9 wajen biyan kudin gidajen haya a 2018

Iyaye, a cikin wata wasika da suka rubuta wa shugaba Buhari, sun bayyana cewa kimanin iyaye 20 daga cikinsu sun mutu yayin da suke jiran dawowar 'ya'yansu.

Gwamnatin tarayya ta yi alkawarin cewa, sauran 'yan matan za su samu ‘yanci bayan masu tayar da kayar baya sun saki 'yan mata 82 bayan musanya da wasu mayakan Boko Haram.

Bayan watanni 5, kungiyar ta sake sakin wasu ‘yan matan Chibok 21.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel