Nigerian news All categories All tags
Hukumar Soji ta Najeriya ta fitar da sanarwa dazun nan kan batun Boko Haram a Magumeri

Hukumar Soji ta Najeriya ta fitar da sanarwa dazun nan kan batun Boko Haram a Magumeri

- Rahotanni a jiya da yau suna ta yawo cewa wai ai Boko Haram ta kace Magumeri

- Sojojin sun karyata wannan batu, inda suka tabbatar sun fatattaki mayakan, suka kuma hallaka da yawa daga cikinsu

- Sun kuma rasa soji 3 da jikkatar wasu 6

Hukumar Soji ta Najeriya ta fitar da sanarwa dazun nan kan batun Boko Haram a Magumeri

Hukumar Soji ta Najeriya ta fitar da sanarwa dazun nan kan batun Boko Haram a Magumeri

Rundunar Sojin Najeriya ta fitar da sanarwar karyata wasu kafafen yada labaru da ke yamadidida cewa wai Boko Haram ta kwace garin Magumeri daga sojin, kuma ta kaa tuta.

Sanarwar, mai sa hannun Kanar Timothy Antigha, mataimakin mai yada labarun jihar, tace wannan batun karya ne, hasali ma, sojin sun baiwa 'yan ta'addar kashi ne sun kuma kore su daji.

DUBA WANNAN: Dakarun Najeriya sunyi kokarin dakile harin Boko Haram a jiya

Ta kuma kara da cewa, Najriya ta rasa soji 3 da raunatar 6 wadanda ake jinya a yanzu, an kuma kwashe gawarwakin masu rasuwar domin sutura.

Ya kuma kara da cewa, niyyar ta mayakan su balle zaman tsaron na yankin yaci tura, an kore su an hallaka da yawa kuma daga cikinsu.

A karshe yayi kira da jama'a su kwantar da hankulansu, kada su bar tsoro ya ratsa su.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel