Nigerian news All categories All tags
Jami'ar ABU ta yaye dalibai 12,000 daga ciki 50 sun fita da digiri mai daraja na daya

Jami'ar ABU ta yaye dalibai 12,000 daga ciki 50 sun fita da digiri mai daraja na daya

- Jami'ar Ahmadu Bello University ta yaye dalibai 12,000

- Dalibai 50 daga ciki sun fita da ajin digiri na farko

- Ana cigaba da gyare-gyaren dakunan dalibai da gina sababbi

Dalibai 12,000 ne suka kammala karatun su na digiri a babbar jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria a yayin da take taron bikin yaye dalibai karo na 40 a jiya. A cikin daliban ne aka samu dalibai masu kwazo 50 wanda suka gama da First class wato digiri mai daraja na daya.

Jami'ar ABU ta yaye dalibai 12,000

Jami'ar ABU ta yaye dalibai 12,000

Mataimakin kansila na jami’ar, Farfesa Ibrahim Garba ya ce jam’iar tana bunkasa yawan daliban da zata dauka nan gaba ta hanyar shigo da sabbin kwasa-kwasai.

A yanzu haka akwai makarantu da yawa da jami'ar ta basu damar samar da karatun digiri da sunan ABU. Sannan kuma an sami karin jami’un da zasu dauki a dinga yin karatun digiri daga gida.

DUBA WANNAN: An yi kicibis da gawar wani dan aji uku a jami'ar ATBU rataye a jikin bishiya

Ana cigaba da gyare-gyaren dakunan dalibai da kuma gina sababbi da dakunan bincike na kimiyya da fasaha.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Yanzu bangaren karatun likitanci ya zama kwaleji mai zaman kansa da shugabanta, hakan zai kara sa a sami dalibai da yawa da zasu yi karatu a fanni daban-daban na harkar asibiti ba lallai likitanci ba.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel