Nigerian news All categories All tags
Najeriya za ta kashe sama da Biliyan 9 wajen biyan kudin gidajen haya a 2018

Najeriya za ta kashe sama da Biliyan 9 wajen biyan kudin gidajen haya a 2018

- An shirya kashe kusan Biliyan 10 wajen biya kudin haya a Najeriya

- Ma’aikatu da dama su na biyan hayan gidaje da shaguna a Kasar

- An dai saba ware Biliyoyin kudi a Kasar wajen biyan kudin haya

Mun samu labari cewa ana shirin kashe kudin da ya kusa kai Naira Biliyan 10 wajen biyan kudin hayan gidaje da ofisoshin manyan Ma’aikatan Kasar nan da kuma Jakadun Kasar a kasashen ketare musamman su Jamus a shekara mai zuwa 2018.

Najeriya za ta kashe sama da Biliyan 9 wajen biyan kudin gidajen haya a 2018

Za a kashe kusan Biliyan 10 wajen biya kudin haya

Jaridar Daily Trust ta bayyana wannan inda mu ka fahimci cewa an ware Naira Biliyan 5 wajen biyan kudin hayar gidajen manyan Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya. Za kuma a kashe wasu sama da Biliyan 4.8 a kan hayar ofisoshin ma’aikatun Kasar da dama.

KU KARANTA: Kasar Saudi za ta fara yi wa masu zuwa ziyara biza

Ministar kudi Kemi Adesoun da bakin ta, take cewa daga shekarar 2012 zuwa 2014 abin da aka kashe wajen biyan kudin haya ya kai Naira Biliyan 3 da rabi. Sai dai ga shi kuma yanzu ana shirin kashe sama da Naira Biliyan 9 a tashi guda a Gwamnati mai-ci.

Akwai dai gidaje kusan 150 na Ma’aikatan Kasar da kuma ofisoshi sama da 232 wanda duk hayar su Gwamnati ta kama. Akwai kuma ofisoshin Jakadun kasar a kasashen waje da gidajen su da ake shirin biya a shekara mai zuwa idan an amince da kasafin kudin kasar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel