Nigerian news All categories All tags
Zaben 2019: Ka nemi gafarar Obasanjo idan kana son tikitin takara a PDP – Inji Jonathan ga Atiku

Zaben 2019: Ka nemi gafarar Obasanjo idan kana son tikitin takara a PDP – Inji Jonathan ga Atiku

- Jonathan ya bukaci Atiku Abubakar ya nemi afuwan Obasanjo idan yana so ya kai labari

- Tsohon shugaban ya shawarci Atiku ya roki Obasanjo idan yana bukatar tikiti na PDP kyauta

- Wasu 'yan takarar shugaban kasa a PDP sun ce ba za su janye wa Atiku ba

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar har yanzu dai akwai sauran rina a kaba a cikin wata yarjejeniyar sirri da jiga-jigan jam’iyyar PDP, yayin da tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan ya bukace shi ya nemi gafarar Cif Olusegun Obasanjo.

Rahotanni sun bayyana a ranar Asabar, 24 ga watan Nuwamba cewa Jonathan ya bukaci Atiku ya roki ko ya nemi afuwar tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo idan yana son samu tikitin takarar shugaban kasa na PDP a shekara ta 2019 kyauta.

Kodayake Obasanjo ya bar siyasa, amma Jonathan yana da ra'ayin cewa har yanzu yana da karfi wajen tsara makomar kasar nan a shekara ta 2019, domin yana da matsayi mai karfi tsakanin masu fada a ji a kasar.

Zaben 2019: Ka nemi gafarar Obasanjo idan kana son tikitin takara a PDP – Inji Jonathan ga Atiku

Tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan

Idan dai baku manta ba tsohon shugaba Jonathan a farkon watan Nuwamban da ta gabata ya shaidawa mawallafin mujallar Ovation a cikin wata hira cewa idan Atiku ya samu tikitin jam’iyyar PDP, babu shaka zai kai ga nasara. Amma dole ne ya nemi afuwan maigidansu, “baba OBJ”.

KU KARANTA: 2019: Atiku sai yayi da gaske don kuwa Sule Lamido ya shirya

Duk da haka babu tabbacin cewa Atiku ya amince da wannan yanayin ko kuma yana shirin fafatawa shi da kansa wajen neman tikitin takarar shugabancin kasar a PDP.

Amma wasu 'yan takarar shugaban kasa a PDP sun ce ba za su janye wa Atiku ba, wanda Jonathan ke kokarin marawa baya.

Majiyar Legit.ng ta tabbatar da cewar, masu neman tikitin jam’iyyar sun kalubalanci Atiku cewa su hadu a bakin daga.

Wadanda ake sa ran sune tsohon gwamna Sule Lamido da tsohon minista Ibrahim Shekarau da gwamna Ibrahim Dankwambo da kuma wani tsohon gwamnan wanda yanzu sanata ne a majalisar tarayya wanda ake sa ran zai bar APC zuwa PDP.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel