Nigerian news All categories All tags
Wanda ya busa usur aka gano kudaden da aka boye a Ikoyi yaki karban Naira miliyan N325m sai dai naira miliyan N860m

Wanda ya busa usur aka gano kudaden da aka boye a Ikoyi yaki karban Naira miliyan N325m sai dai naira miliyan N860m

- Mutumin da busa usur din sa yasa hukumar EFCC ta gano kudaden da aka boye a Ikoyi ya ce bai zai ansa kasa da kashi biyar ba a matsayyin la'ada

- Busa usur din mutum yasa aka gano naira biliyan N13bn a cikin wani gida a Ikoyi

- Gwamnatin tarraya ta yi alkwarin biya duk wanda ya busa usur aka gano kudadden gwamnati da aka sace kashi 5% daga cikin kudin

Wanda ya busa usur din da yasa aka gano wasu makudan kudaden da aka boye a Ikoyi yaki karban Naira miliyan N325m a matsayin la’ada, sai dai naira miliyan N860m

Mutumin wanda busa usur din sa yasa hukumar EFCC ta gano kudaden da aka boye a wani gida dake unguwar Ikoyi a jihar Legas yayi ikirarin cewa ba zai ansa kasa da kashi 5% ba daga cikin kudaden da aka gano ba.

Busar usur din da mutumin yayi, ya taimakawa hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC ta gano dala milyan $43m, wanda yayi daidai da naira biliyan N13bn a kudin Najeriya daga wata gida a ikoyi.

Wanda ya busa usur aka gano kudaden da aka boye a Ikoyi yaki karban Naira miliyan N325m sai dai naira mlyan N860m

Wanda ya busa usur aka gano kudaden da aka boye a Ikoyi yaki karban Naira miliyan N325m sai dai naira mlyan N860m

Gwamntin Najeriya ta yi alkwarin biyan duk wanda yaba da rahoto da ya taimaka aka gano inda aka boye kudaden gwamnati da aka sace, za a bashi kashi biyar daga cikin kudaden.

KU KARANTA : Na fada wa Buhari halin da talakawa suke ciki – Sheikh Bala Lau

Mutumin da ya busa usur din Ikoyi yayi ikrarin cewa ba zai anshi naira miliyan 325m, sai dai miliyan 860m kamar yadda aka mi shi alkawari.

Mai ba wa fadar shugaban kasa shawara a fannin cin hanci da rashawa ferfesa Bolaji Owasanoye, ya ce idan kudaden da aka gano suna da yawa kashin yana raguwa amma idan kudaden basu da yawa sosai kashin da za a ba wanda ya busa usur din zai karu, wannan shine aihin tsarin da ake bi a duniya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel