Nigerian news All categories All tags
Ganduje ya yi kira ga kamfanoni masu zaman kansu da bada hadin gwiwa don bunkasa tattalin arziki

Ganduje ya yi kira ga kamfanoni masu zaman kansu da bada hadin gwiwa don bunkasa tattalin arziki

- Gwamnan Kano ya yi kira ga kamfanoni masu zaman kansu su bada hadin gwiwa don bunkasa tattalin arziki

- An bude filin baje-koli a jihar Kano

- Najeriya na kokarin daina dogaro da man fetur

Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya yi kira ga yanki kamfanoni masu zaman kansu da su hada gwiwa da gwamnatin jihar don farfado da tatalin arzikin kasa.

Ganduje ya yi wannan kiran ne a Kano a yayin da yake kaddamar da bude filin baje-koli karo na 38 a jihar.

Ganduje ya yi kira ga kamfanoni masu zaman kansu don bunkasa tattalin arziki

Gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje

Gwamnan yaa ce a shirye gwamnatin sa take da ta samar wa da ‘yan kasuwa wadataccen wuri da bangare da zasu taimaka a cikin wani yanki na tattalin arziki.

Gwamnan ya shaida cewa duk yana cikin shawarwarin da aka yanke don fadada cikin garin Kano, ana gina gadar sama da ta kasa da zata saukaka cinkoson ababen hawa.

Hukumar KACCIMA ce ta wallafa shirin domin yana daya daga cikin tsarin cigaba a kasa. Ya kuma yabawa hukumar KACCIMA da hada wannan babban baje-koli domin kuwa zai kawo cigaban arziki a jihar.

Shugaban KACCIMA, Alhaji Dalhatu Abubakar ya jinjinawa gwwamnatin tarayya kan jajircewar da tayi don ganin kasa ta daina dogaro a kan man fetur kadai.

DUBA WANNAN: Wani dan sanda ya kira ruwa bayan ya kwaci N40,000 a hannun wani da ya kama

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

‘Manya da kananan sana’o’i suna daya daga cikin abubuwan da suke bunkasa arzikin kasashe da yawa, don haka ya kamata Najeriya ta zage damtse wajen ganin ta farfado da sana’o’i da zasu taimaka a cigaban tattalin arzikin kasa’ Alhaji Dalhatu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel