Nigerian news All categories All tags
2019: Alhaji Atiku Abubakar zai koma Jam’iyyar PDP a yau

2019: Alhaji Atiku Abubakar zai koma Jam’iyyar PDP a yau

- Ana tunani Atiku Abubakar na shirin dawowa PDP yau

- Kwanan nan ne Atiku ya bar Jam’iyyar APC mai mulki

- Da alamu Atiku zai nemi takarar Shugaban Kasa a PDP

Kwanaki Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Alhaji Atiku Abubakar ya bar Jam’iyyar APC. Sai dai bisa dukkan alamu za a samu sabon rikici a Jam’iyyar idan har Atiku Abubakar ya dawo Jam'iyyar PDP.

2019: Alhaji Atiku Abubakar zai koma Jam’iyyar PDP a yau

Atiku Abubakar ya fice daga Jam'iyyar APC

Jaridar Punch ta rahoto cewa yau ake sa rai Atiku Abubakar ya karbi katin zama ‘Dan Jam’iyyar PDP a Kauyen san a Jada. A karshen makon nan ne tarin Jama’a su ka tarbi Waziri Atiku a Garin Yola bayan ya fice daga Jam’iyyar APC mai mulki a Kasar.

KU KARANTA: Jam’iyyar PDP tace za ta karbi Atiku da hannu biyu-biyu

Mr. Ahmed Lawan wani na kusa da Atiku wanda yana cikin manyan Jam’iyyar APC ya tabbatar da wannan. Haka kuma Umar Ardo, wani babba a Jam’iyyar PDP mai adawa a Jihar Adamawa yace Atiku ya shirya komawa tsohuwar Jam’iyyar sa.

Atiku zai dawo Jam’iyyar ne domin ya samu tsayawa takarar Shugaban Kasa a 2019. Sai dai komawar Atiku zuwa Jam’iyyar zai kawo wani sabon rikici. Sauran masu neman kujerar PDP irin su Sule Lamido sun shirya yaki da Atiku a zaben 2019.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel