Nigerian news All categories All tags
Wata kungiya ta bayyana daliliai 8 da yasa Atiku ba zai taba yin shugabancin Najeriya ba

Wata kungiya ta bayyana daliliai 8 da yasa Atiku ba zai taba yin shugabancin Najeriya ba

- Wata kungiya mai zaman kanta ta bayyana daliliai yasa Atiku ba zai yin shugabancin Najeriya ba

- Kungiyar ta nuna goyoyn bayan ta shugaban kasa Muhammadu Buhari

- Kungiyar ta ce rashin hangen nesa da rashin akida yana daga cikin matsalolin siyasar Atiku

Wata kungiyar yan Najeriya dake kasar Birtaniya wanda ke wayar da kan alumma akan illar cin hanci da rashawa (NACA), ta ce Atiku ba zai taba zama shugaban kasar Najeriya ba.

Kungiyar ta bayyana haka ne ta shafinta na tuwita mai suna @CorruptConcern, inda ta yi ikrarin cewa tana da mabiya dubu goma sha takwas 18,000.

Wata kungiya ta bayyana daliliai 8 da yasa Atiku ba zai taba yin shugabancin Najeriya ba

Wata kungiya ta bayyana daliliai 8 da yasa Atiku ba zai taba yin shugabancin Najeriya ba

Kungiyar wanda ta nuna goyon bayan ta ga shugaban kasa Muhammadu Buhari ta bayyana dalilai takwas 8 da zai sa yan Najeriya su ki zaben Atiku a 2019.

KU KARANTA : An nada tsohon shugaban tsagerun Neja delta Ateke Tom sarkin garin Okorichi a jihar Rivas

1. Neman shugabancin ruwa a jallo

2. Rashin biyayya wajen neman shugabanci

3. Almundahana da kudin al’umma

4. Yadda ya samu arzikin sa a lokacin da yake aiki a hukumar fasa kwabri (Nigerian Custom Service)

5. Kasancewar sa a cikin wadanda suka lalata tattalin arzikin Najeriya

6. Rashin hangen nesa

7. Rashin akida

8. Karuwan dan siyasa

A ranar juma’a ne shaharren lauyan Najeriya Festus Keyamu ya soki Atiku akan rashin fadawa yan Najeriya aininhin dalilin da yasa ya fice daga jam’iyyar APC.

Festus keyamu ya ce tsohon mataimakin shugaba kasa ya fita daga jam’iyyar APC ne saboda yasan samu tikitin takara zai yi masa wuya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel