Nigerian news All categories All tags
2019: Atiku sai yayi da gaske don kuwa Sule Lamido ya shirya

2019: Atiku sai yayi da gaske don kuwa Sule Lamido ya shirya

- Sule Lamido ya tara Jama’a wajen bude ofishin Jam’iyyar PDP

- Dubban Jama’a sun fito tarbar tsohon Gwamnan na su a Ringim

- Lamido yana cikin wadanda su ke neman Shugaban Kasa a 2019

Mun samu labari daga Jaridar Rariya cewa tsohon Gwamnan Jigawa Alhaji Sule Lamido ya tara cincirondon mabiya a Garin Ringim da ke Jihar Jigawa.

2019: Atiku sai yayi da gaske don kuwa Sule Lamido ya shirya

Tsohon Gwamna Sule Lamido a Garin Ringim

Kamar yadda mu ka fahimta Alhaji Sule Lamido ya tadawa masu neman takarar Shugaban Kasa hankali bayan da ya tara makudan Jama’a wajen taron bude ofishin Jam’iyyar PDP mai adawa a Masarautar Ringim da ke Jihar jigawa.

KU KARANTA: Su Sule Lamido za su buga da Atiku Abubakar a PDP

Tsohon Gwamna Sule Lamido ya tara dubban mutane a Garin Ringim inda wasu su kace ba shakka za a buga da shi a wajen neman kujerar Shugaban Kasar a zabe mai zuwa. Lamido yana cikin wadanda su ka ki barin Jam’iyyar PDP.

Yanzu haka dai Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Alhaji Atiku Abubakar ya fice daga Jam’iyyar APC. Ana tunani Atiku zai koma PDP ne amma masu neman kujerar PDP irin su Sule Lamido sun shirya yaki da Atiku wajen neman tikitin Jam’iyar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel