Nigerian news All categories All tags
CBN ya kashe Naira biliyan 6 wajen gina tsangayar koyar da ilimin kasuwanci a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria

CBN ya kashe Naira biliyan 6 wajen gina tsangayar koyar da ilimin kasuwanci a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria

Babban bankin najeria CBN ya kashe naira biliyan 6 domin samar da tsangayar koyar da ilimin kasuwanci a jamiar Ahmadu bello drake Zaria a jihar kaduna.

Da yake karin haske, mataimakin shugaban jami'ar, Malam garba Shehu, yayin bikin yaye dalibai kashi na 40 a Samaru ya ce tsangayar ta fara ne a sashen koyar da ilmin Akawu, kasuwanci da kuma tsimi da tanadi.

CBN ya kashe Naira biliyan 6 wajen gina tsangayar koyar da ilimin kasuwanci a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria

CBN ya kashe Naira biliyan 6 wajen gina tsangayar koyar da ilimin kasuwanci a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria

Har ila yau mataimakin yace wannan cigaban ya samarda karin bunkasa sashe sashen jamiar da kuma kirkiro wasu sabbin sassa irin wadannan fannoni. Ya kuma kara da cewa sashen koyar da aikin likita an bunkasa shi zuwa babbar kwaleji ta koyon a ikin likita da rassa guda 4. Haka kuma cigaban zai samar da wasu karin fannoni 3 a sabon shekarar karatu ta 2017/2018. fannoni sun hadar da kimiyyar aikin hakori, kimiyar gwaje gwaje da kuma kimiyar gano cutuka ta manhajar komfuta.

DUBA WANNAN: An yi kicibis da gawar wani dan aji uku a jami'ar ATBU rataye a jikin bishiya

Haka kuma mataimakin yace jamiar ta samar da manhajar daukan darusa ta yamar gizo don rage cunkoson dalibai. Tsarin Daukar darussa ta manhajar komfuta yana tafiya ne daidai da zamani. Mataimakin ya ce a shekarar da ta gabatane jami'ar ta kirkiro wasu sabbin fannoni a sashen koyon aikin injiniya, kuma jami'ar na kokarin sake kirkiro wasu sabbin fannoni da dama domain koyarwa a guraben da take dasu.

A nasa bangaren babban daraktan NNPC, Maikanti Baru, ya yabawa wasu dalibai su kimanin 50 da suka fita da sakamako mafi daraja a fannoni daban-daban. Sannan ya bayar da tallafin karatu ga wani dalibi, Al'amin Bugaji, wanda ya samu maki 4.93 har ya zuwa matakin karatu na karshe wato digiri na uku.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel