Nigerian news All categories All tags
Atiku ba zai ba mu tsoro ba Inji masu neman takara a Jam’iyyar PDP

Atiku ba zai ba mu tsoro ba Inji masu neman takara a Jam’iyyar PDP

- Ana tunani Atiku Abubakar na shirin dawowa Jam’iyyar PDP

- Masu neman Shugaban Kasa a Jam’iyyar sun ce sai dai a buga

- Da alamu idan Atiku ya dawo PDP ba zai samu tikiti a banza ba

A karshen makon can ne Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Alhaji Atiku Abubakar ya fice daga Jam’iyyar APC. Malam Ibrahim Shekarau da sauran masu neman kujerar PDP irin su Sule Lamido sun shirya yaki da Atiku idan zai dawo Jam’iyyar Inji Daily Trust.

Atiku ba zai ba mu tsoro ba Inji masu neman takara a Jam’iyyar PDP

Shekarau yana neman Shugabanci a Jam’iyyar PDP

Ana sa rai kwanan nan Atiku zai yanki takardar shiga Jam’iyyar PDP mai adawa a kauyen sa kwanan nan domin ya samu tsayawa takarar Shugaban Kasa a Jam’iyyar ta PDP a zaben 2019. Jam’iyyar tace za ta karbe sa da hannu biyu-biyu inda ya dawo.

KU KARANTA: Ku na gani cewa akwai wadanda za su bi Atiku?

Sai dai masu shirin tsayawa takarar Shugaban Kasa a Jamiyyar a 2019 irin su Malam Ibrahim Shekarau da Sule Lamido fa sun ce don Atiku ya dawo PDP, ba za su janye ko su fasa tsayawa takarar su ba don kuwa sai dai a buga a san nayi a zaben mai zuwa.

Shi ma Sule Lamido yace ba zai ce komai ba sai Atiku ya tabbatar da cewa ya dawo Jam’iyyar. ‘Yan takarar dai sun ce ba su ji tsoron kowa kuma babu wanda zai samu tikitin a sama don kuwa sai an buga wajen neman kujerar Shugaban kasa a 2019.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel