Nigerian news All categories All tags
Canza sheka: Ba dani za a yi ta ba, a nan bana tare da Atiku – Inji gwamnan Adamawa

Canza sheka: Ba dani za a yi ta ba, a nan bana tare da Atiku – Inji gwamnan Adamawa

- Gwamnan jihar Adamawa ya ce yana nan daram a APC bayan ficewar mai gidansa daga jam’iyyar

- Gwamnan Bindow da ministan harkokin mata na gaba-gaba cikin wadanda ake zato zasu bi Atiku

- Kwamishinan labarai na jihar ya ce an zabi gwamnan ne a karkashin jam’iyya APC kuma zai ci gaba da kasancewa ciki

Kalubale na farko biyo bayan ficewar Atiku Abubakar daga APC ya zo ne a karshen makon nan, lokacin da gwamnan jihar Adamawa, Jibrilla Bindow ya ce ba shi da wani shiri na barin jam’iyyar sakamakon ficewar gidansa.

Bindow da Aisha Alhassan, ministan harkokin mata, wadanda tuni sun yi alkawalin yin biyayya ga Atiku, da sauransu, sun kasance daga cikin sunayen manyan ‘ya’yan jam”iyyar APC da ake zato zasu bi sahun tsohon mataimakin shugaban kasar.

Duk da haka, gwamna ya ce dangantakarsa da tsohon mataimakin shugaban zai kasance mai dadi da kuma dacewa da juna don makomar gaba.

Canza sheka: Ba dani za a yi ta ba, a nan bana tare da Atiku – Inji gwamnan Adamawa

Gwamnan jihar Adamawa, Jibrilla Bindow

"An zabi gwamnan a karkashin jam’iyya mai mulki ta APC kuma zai ci gaba da kasancewa a matsayin gwamnan APC", kwamishinan labarai na jihar Adamawa, Ahmed Sajoh, ya shaidawa majiyar Legit.ng a ranar Asabar, 25 ga watan Nuwamba.

KU KARANTA: Gargadi ga Buhari: Sanata Shehu Sani ya bayyana abinda zai faru a jam'iyyar APC sakamakon ficewar Atiku

Sajoh ya ce shugaban jam'iyyar APC wanda ya damu matuka da ficewar Atiku daga jam’iyyar a safiyar ranar Juma’a, ya bayyana cewa, kada ya ji tsoro ko damuwa da batun.

Har zuwa yanzu Atiku bai bayyana ko wane jam’iyyun adawa ne zai koma ba, amma shawarwari sun yi nuni da cewa ya yanke shawarar shiga PDP, wanda ya bayyana a fili a cikin 'yan watanni.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel