Nigerian news All categories All tags
Ka fice kai kadai: Gwamnanonin APC sun yi baran-baran da Atiku

Ka fice kai kadai: Gwamnanonin APC sun yi baran-baran da Atiku

- Wasu Gwamnoni na APC sun ce ba su tare da Atiku Abubakar

- Atiku ya fice daga Jam’iyyar APC mai mulki makon kwanan nan

- Gwamnonin dai sun ce sam ba su yi mamakin abin da ya faru ba

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Alhaji Atiku Abubakar ya fice daga Jam’iyyar APC mai mulki a karshen makon kwanan da ta wuce inda yace Jam’iyyar ta kama hanyar mutuwa.

Ka fice kai kadai: Gwamnanonin APC sun yi baran-baran da Atiku

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku ya bar APC

Bayan ficewar Atiku daga Jam’iyyar APC mai mulki, Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai ya tabbatar da cewa babu Gwamnan jam’iyyar da zai bar ta ya bi tsohon Mataimakin Shugaban Kasar. Da alamu kuma dai haka aka yi a ayanzu.

KU KARANTA: Mutane 4 da za su iya bin Atiku bayan ya fice daga PDP

Gwamnan Jihar Adamawa wanda daga nan Atiku ya fito watau Jibralla Bindow ya bayyana cewa shi yana nan a Jam’iyyar APC babu gudu babu ja da baya. A baya dai Bindow yana tare da Alhaji Atiku Abubakar. Wasu ‘Yan PDP dai sun fara zawarcin Atiku.

Haka kuma Gwamnan Jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya bayana cewa sam abin da Atiku yayi bai ba su wani mamaki ba. Ganduje yace ba zai yi mamaki idan Atiku ya koma wata Jam’iyya wanda ba PDP ba. Gwamna Ganduje yace siyasa rigar ‘yanci ce.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel