Nigerian news All categories All tags
Shin me yasa Nasir El-Rufai ya qi jinin Atiku Abubakar tsohon VP?

Shin me yasa Nasir El-Rufai ya qi jinin Atiku Abubakar tsohon VP?

- A baya Elrufai yaron Atiku ne a siyasance

- Tunda aka sami matsala tsakanin Obasanjo da Atiku, Nasir ya koma gidan Obasanjo

- Kujera daya suke hari, shekaru goma kenan

Shin me yasa Nasir El-Rufai ya qi jinin Atiku Abubakar tsohon VP?

Shin me yasa Nasir El-Rufai ya qi jinin Atiku Abubakar tsohon VP?

Gwamnan Kaduna Malam Nasir Ahmad El-Rufai, ya ki jinin siyasar Atiku Abubakar, tsohon mataimakin Obasanjo a PDP, kuma duk wata dama da tazo, baya bari ta wuce sai ya caccaki Atikun, ko da ba'a ko gatsal.

Shin to meye Atikun yayi wa Malam din ne? A binciken mu dai, Legit.ng ta gano muku dalilai da dama, ku biyo mu.

DUBA WANNAN: Boko Haram ta sake kwace Magumeri

Shidai Atiku yana so ya zama shugaban kasa shekaru kusan 20 kenan, tun yana tare da Shehu Yaraduwa marigayi. Shima kuma Nasir Elrufai daga shekaru 10 zuwa yanzu yana sha'awar kujerar.

A aikin da suka yi tare, Malam Nasir a littafinsa 'The Accidental Public Servant'ya zargi Atikun da son cin rashawa da satar kudaden gwamnati, da kin bin ka'idar aiki. Shi kuma Atiku a nasa littain 'My Life', ya ce bai taba sata ko cin hanci ba, aiki tukuru ya tara masa dimbin dukiyarsa.

El-Rufai ya ki jinin Atiku saboda a cewarsa, dan tamore ne, wato opportunist a turance, shi kuwa Atiku, ya ce shi taimakon talakawa ya sanya a gaba.

Atiku ya sha shiga kotu don kare kansa daga manyan zarge zarge, da ma cin zali idan an rufe masa kamunnansa na kasuwanci, ko a kwanan nan Intels dinsa ta shiga tasku hannun NPA, wadda ake gani aikin Elruffai ne na tatse dan siyasar don kada ya sami damar taka rawa a 2019.

El-Rufai dai ya taba yin gudun hijira saboda zaluncin gwamnati da yace tsohuwar gwamnatin Yaraduwa da ya taimaka aka kafa ta yi masa, wanda ya kira da Kafiri mai bin akidar gurguzu da Atishanci a lokacin yana dalibi a ABU Zaria.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel