Nigerian news All categories All tags
Duk ranar Talata da Laraba sai mahaifina ya kwana dani – Wata yar shekara 12

Duk ranar Talata da Laraba sai mahaifina ya kwana dani – Wata yar shekara 12

- Wata karamar yarinya ta sanar da kotu cewa mahaifinta yana kwana da ita

- Bincike ya nuna mahaifn yarinyar ya saki mahaifiyarta a shekaru uku da suka gabata

- Kotu ta ba da belin mai lafin akan naira N200,000

Wata karamar yarinya mai shekaru goma sha biyu 12 ta sanar da kotun majistare dake jihar Legas, cewa mahaifinta mai suna Idoko yana tilasta ta, ta kwana da shi a duk ranar Talata da Laraba a gidan su.

Bincike ya nuna cewa Idoko ya saki matar sa kuma mahaifiyar yarinyar a shekaru uku da suka gabata, kuma ya hana ta tafiyar da diyar a lokacin tana yar shekara 9.

Duk ranar Talata da Laraba sai mahaifina ya kwana dani – Wata ‘yar shekara 12

Duk ranar Talata da Laraba sai mahaifina ya kwana dani – Wata ‘yar shekara 12

Daganan ya fara ma diyar sa fyade har ya kai da, a duk ranar Talata da Laraba sai ya kwanta da ita.

KU KARANTA : Gargadi ga Buhari: Sanata Shehu Sani ya bayyana abinda zai faru a jam'iyyar APC sakamakon ficewar Atiku

Jami’an yansadar jihar Legas sun shigar da karar mahaifin yarinyar a kotu bisa zargin aikata laifin alfasha da diyar cikin sa, wanda yin haka ya saba wa dokar kare hakkin kanana yara a Najeriya.

Kotu ta daga sauraron karar zuwa 12 ga wata Disamba na shekara 2017, kuma ta ba da belin Idoko akan naira N200,000.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel