Nigerian news All categories All tags
Gwarzon Dalibin da ya gama Digiri da maki 4.93 cikin 5.00 ya samu kyauta daga NNPC

Gwarzon Dalibin da ya gama Digiri da maki 4.93 cikin 5.00 ya samu kyauta daga NNPC

- Al-Ameen Bugaje ya gama Jami’ar da matakin da ya fi na kowa

- Bugaje ya samu kyauta daga kamfanin mai na kasa watau NNPC

- Wannan hazikin matashi ya gama karatu da maki 4.93 cikin 5.0

Mun samu labari cewa Hukumar NNPC ta dauki nauyin karatun Dalibin nan da ya zama zakaran gwajin dafi a Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya wannan shekarar.

Gwarzon Dalibin da ya gama Digiri da maki 4.93 cikin 5.00 ya samu kyauta daga NNPC

Al-Ameen Bugaje ya samu gudumuwa daga NNPC

Hukumar NNPC za ta dauki nauyin karatun Dalibin da ya kammala Digiri da maki 4.93 cikin 5.00 a Ahmadu Bello ta Zariya da aka yaye jiya mai suna Al-Ameen Bugaje a ko ina yake sha’awa a fadin Duniya kamar yadda mu ka samu labari jiya.

KU KARANTA: Hazikin ‘Dalibi daga Jihar Katsina ya gama Jami’a da makin kare dangi

A cikin wadanda su ka gama da matakin da ya fi na kowa Al-Ameen Bugaje ne a sama wanda yayi Digiri a ilmin zama Injiniyan wuta. Shugaban Hukumar NNPC Dr. Maikanti Baru yace Kamfannin NNPC za ta biya masa kudin karatun Digiri na 2 da 3.

Maikanti Baru, wanda shi ma a Jami’ar ta Ahmadu Bello ta Zariya yayi karatun zama Injiniya kuma ya fita da irin matakin wannan Dalibi. Baru yace duk inda wannan haziki yake so yayi karatu a Duniya har zuwa matakin PhD, an dauke masa nauyi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel