Nigerian news All categories All tags
Zaben 2019: Ba na tunanin shugabancin Najeriya yanzu – Inji Makarfi

Zaben 2019: Ba na tunanin shugabancin Najeriya yanzu – Inji Makarfi

- Sanata Ahmed Makarfi ya nizanci kansa daga shugabancin Najeriya

- Makarfi ya ce ba ya tunanin neman shugabancin kasar a wannan lokaci

- Shugaban PDP ya ce ya kamata ana sani cewa mulki daga Allah ne

Shugaban babban jam’iyyar adawa ta PDP, sanata Ahmed Makarfi a tattaunawarsa da jaridar PUNCH ya bayyana cewa a wannan lokacin, ba ya tunanin neman shugabancin kasar, musamman ma idan ya yi la’akari da duk matsaloli da ke kansa.

Kamar yadda Legit.ng ke da labari, shugaban ya ce babban fifiko shine ya gudanar da taron kolin jam’iyya kuma tabbatar da cewa an yi wa kowane dan takara adalci kamar yadda tsarin mulkin jam’iyyar PDP ta tanada.

Da yake tofa albarkacin bakinsa ga shugabancin jam’iyyarsa, Makarfi ya ce bai yi nadamar amince ya jagoranci jam’iyyar ba.

Zaben 2019: Ba na tunanin shugabancin Najeriya yanzu – Inji Makarfi

Shugaban babban jam’iyyar adawa ta PDP, sanata Ahmed Makarfi

Ya ce tabbas, za a sami ra’ayoyi daban-daban yayin da suke kusantar taron jam’iyyar saboda zaben 2019. Ya ci gaba da cewa, “Ya kamata mutane su sani cewa mulki daga Allah ne. Babu wani nasara da za mu iya yi idan ba nufin Allah bane. Za mu kasance masu gaskiya da tabbatar da adalci ga kowane dan takara”.

KU KARANTA: Shugaba Buhari bai damu da samun tikitin takara kyauta ba - Tsohon Gwamna

“Mun kuma gaya musu cewa a duk lokacin da suka ga munyi kuskure, sai su zo su tattauna tare da mu, za mu gyara, ba wai yin zarge-zarge maimakon tattauna da mu ba, irin wanna ba zai ciyar da jam’iyyar gaba ba”, inji shi.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel