Nigerian news All categories All tags
Yanzu-yanzu: Boko Haram ta kwace garin Magumeri a jihar Borno

Yanzu-yanzu: Boko Haram ta kwace garin Magumeri a jihar Borno

- Tun da damina ta dauke Boko Haram suka kara kaimi wajen kai hare-hare

- Dama a kwanakin baya sun kai hari a garin sun kashe mutane shida sun kona gidaje

- Hukumar soji ta tabbatar da lamarin amma bata baiyan cewa sun kwace garin ba

Wasu wadanda ake zargi da mayakan Boko Haram ne sun kwace garin Magumeri da ke arewa maso yammacin Maiduguri, babban birnin jihar Borno, kamar yadda rahotanni suka baiyana.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ce mutanen garin Magumeri sun shaida musu ta wayar salula cewa sun arce zuwa wani daji da ke kusa da su.

Boko Haram ta kwace garin Mugemiri a jihar Borno

Boko Haram ta kwace garin Mugemiri a jihar Borno Hoto: Getty Images

Wata majiyar soji ta bada tabbacin cewa an kai hari garin, amma ba ta yi bayani game da ko maharan sun kwace garin ba.

A farkon watan da mu ke ciki ne, aka kashe mutum shida tare da kone gidaje masu yawa a harin da aka kai garin.

Mayakan Boko Haram sun kara zafafa hare haren da suke kai wa tun bayan daukewar ruwan sama a watan Satumba.

DUBA WANNAN: Shugaba Buhari bai damu da samun tikitin takara kyauta ba - Orji Kalu

Wannan shi ne hari na baya bayanan tun bayan harin kunar bakin wake da aka kai a wani masallaci a jihar Adamawa, inda mutum 50 suka hallaka.

Harin na cikin hare hare mafi ya muni da aka kai tun bayan da Shugaba Muhammadu Buhari ya hau kan mulki a shekarar 2015, inda ya yi alkawarin kawo karshen masu tada kayar baya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, a tuntube mu a:

labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel