Nigerian news All categories All tags
Kungiyar Afenifere ta zargi Tinubu da yunkurin fitowa takara a zaben 2019

Kungiyar Afenifere ta zargi Tinubu da yunkurin fitowa takara a zaben 2019

- Tinubu ya kai ma shugaban kungiyar Afenifere Pa Reuben Fasoranti ziyara a gidan sa dake Akure

- Kungiyar Afenifere ta ce ziyarar da Tinubu ya kaima Pa Reuben Fasoranti gidan sa ba shi da alaka da siyasa

- Tinubu ya ziyarci Pa Reuben Fasoranti ne dan karfafar dangantakar sa da kungiyar inji Agboola

Kungiyar yarbawan Najeriya, Afenifere, ta ce bata da wata masaniya akan kudirin takarar jagorar jam’iyyar APC Bola Ahmed Tinubu a zaben 2019.

Kungiyar Afenifere ta zargi Tinubu da yunkurin fitowa takara a zaben 2019

Kungiyar Afenifere ta zargi Tinubu da yunkurin fitowa takara a zaben 2019

Afenifere ta ce ziyarar da Tinubu ya kai ma shugaban kungiyar Afenifere, Pa Reuben Fasoranti, a gidan sa dake Akure babban birnin Ondo ba shi da alaka da siyasa.

Kungiyar ta yi wannan sanarwar ne ta mai magana da yawun bakin ta, Sehinde Arogbofa, inda ya bayyana cewa Tinubu da Pa Reuben sun yi ganawar sirri da juna amma bashi da wani alaka da siyasa.

KU KARANTA : Abu guda yasa Atiku ya bar jam’iyyar APC - Festus Keyamo

Arogbof ya ce “Mutane za su iya fasara ziyarar da Tinubu ya kai wa shugaban kungiyar Afenifere yadda suka ga dama, amma ba mu da wata masaniya akan takarar Tinubu a zaben 2019.

“Dangantakar Tinubu da kungiyar Afenifere a shekaru 15 da suka gabata ya ragu, shiyasa yake son ya karfafa alakar sa da kungiyar, kuma ya zama dole mu ya ba mishi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel