Nigerian news All categories All tags
Illoli 12 na amfani da abincin gwan-gwani

Illoli 12 na amfani da abincin gwan-gwani

Mafi yawan abincin gwangwani da ake saye a manyan kantunan suna kunshe da sunadarai dake kawo lahani tare da cutar da lafiyar dan Adam. Don haka, me yasa ba zamu guji waɗannan kayan abinci ba mu komawa na halitta waɗanda suke tsarkaka.

Binciken Legit.ng a yau ya kawo muku illoli 12 dake tattare wajen amfani da abincin gwan-gwani sakamakon sunadarai da suka kunsa dake kawo zagon kasa ga lafiyar mu.

Abincin gwan-gwani

Abincin gwan-gwani

Binciken masana kiwon lafiya ya jeranto cututtuka da sunadaran cikin abincin gwam-gwani ke sanyawa a jikin dan Adam kamar haka:

1. Cuttukan zuciya

2. Ciwon ƙoda

3. Cutar daji ta mama na mata

4. Sanya nauyin jiki da teɓa

5. Ciwon Suga

6. Cututtukan gaba na maza da mata

7. Cutar mutuwar ɓarin jiki

8. Cututtukan fata da na ido

9. Tashin zuciya, ƙwarnafi, amai da gudawa

10. Cutar daji ta ƙwaƙwalwa

11. Cutar Asma

12. Kawo matsaloli wajen mata masu ciki da kuma haihuwa

KARANTA KUMA: Hukumar EFCC ta kama kadarori 3 na tsohon gwamnan jihar Benue

Ire-iren waɗannan kayan abinci na gwan-gwani su hadar da: lemun gwan-gwani, ganyeyyaki na gwan-gwani, ababen sha na gwan-gwani, miyar gwan-gwani, tumatirin gwan-gwani, kifin gwan-gwani, waken gwan-gwani, nama na gwan-gwani da makamantansu

LATSA WANNAN: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel