Nigerian news All categories All tags
Jami’an sojin sama su 50 sun samu karin girma na musamman

Jami’an sojin sama su 50 sun samu karin girma na musamman

- Rundunar sojin sama ta Najeriya ta yi wa wasu jami’an ta karin girma na musamman

- Babban hafsan sojin sama ya yi wa manyan jami'ai ado tare da matansu

- Rundunar sojin Najeriya ta ce tana yin irin wannan karin girma kowace shekara don motsa jami'an

Rundunar sojin sama ta Najeriya (NAF) a ranar Asabar ta yi wa wasu jami’an ta ado wanda suka hada da Air Vice Marshals (AVMs), 22 da Air Commodores 28 wadanda rundunar ta yi wa karin girma na musamman.

Wannan shi ne karo na farko da rundunar ta yi irin wannan karin girman.Har ila yau, cikin wadanda aka yi wa ado ya hada da marigayi Air Commodore Gabriel Ochai wanda Allah ya yi wa rasuwa sakamakon wani hadarin jirgin sama a ranar 24 ga Agusta 2017 a Kaduna. Matarsa, Mrs. Rita Ochai, ta halarci taron don karɓar matsayi a madadin mijinta.

Babban hafsan sojin sama, Air Marshal Sadiki Abubakar, wanda ya yi wa manyan jami'ai ado tare da matansu da kuma wasu manyan mutane, ya bayyana cewa, karin girma ga manyan jami'an ta biyo bayan kyakkyawan ayyukan da suka a baya.

Jami’an sojin sama su 50 sun samu karin girma na musamman

Babban hafsan sojin sama, Air Marshal Sadiki Abubakar

Kamar yadda Legit.ng ke da labari, Air Marshal Abubakar ya taya sabbin shugabannin da iyalansu murna yayin da ya shawarce su da su sadaukar da kai ga ayyukansu don tabbatar da muhimmancin darajar da aka san NAF da ita.

KU KARANTA: Mutum guda ya shiga hannu da laifin kisan Sakataren jam'iyyar APC

Tun da farko a cikin jawabinsa na maraba, shugaban gudanarwa (COA), Air Vice Marshal Lawal Alao, ya bayyana cewa, rundunar sojin Najeriya a kowace shekara tana yin irin wannan karin girma don motsa jami'an.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel