Nigerian news All categories All tags
Wani Dalibi ya kammala Digiri da maki 4.93 cikin 5.00 a ABU Zaria

Wani Dalibi ya kammala Digiri da maki 4.93 cikin 5.00 a ABU Zaria

- Wani Dalibi ya lashe komai a Jami’ar ABU ta Zariya

- Al-Ameen Bugaje ya zama gwarzon wannan shekara

- Bugaje ya gama Digiri da maki 4.93 cikin maki 5.0

Mun samu labari cewa babbar an samu wani ‘Dalibi da ya kammala Digiri da maki 4.93 cikin 5.00 a Ahmadu Bello ta Zariya a yau da aka yaye Dalibai.

Wani Dalibi ya kammala Digiri da maki 4.93 cikin 5.00 a ABU Zaria

Hoton Al-ameen Bugaje tare da 'Dan uwan sa Idris Bugaje daga Facebook

Al-Ameen Basheer Bugaje ya gama Jami’ar ne da mataki na farko inda sakamakon sa ya zarce na kawo a kaf fadin Jami’ar da ta ke cikin manya a Kasar. Al-Ameen Bugaje yayi Digiri ne a fannin kanikanci na harkar lantarki. A bana dai wannan dalibi ne gwarzon Jami’ar.

KU KARANTA: Wani Malamin Jami'a yayi wa wata mata fyade

Wani Dalibi ya kammala Digiri da maki 4.93 cikin 5.00 a ABU Zaria

Al-Ameen Bugaje ya kafa tarihi a ABU Zaria

An kawo sunan Al-Ameen cikin hazikan wannan shekarar tare da wasu irin-sa. A wannan karo an samu wadanda su ka ciri tuta a Makarantar inda aka samu wadanda su ka fita da matakin farko a kwas din da ba a saba ba irin su harkar tattali da ilmin sindaran da ke jikin mutum.

Al-Ameen ya fito ne daga Jihar Katsina amma mutanen gidan su Malaman Jami’a ne kamar yadda mu ka samu labari. Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya ta yaye Dalibai 8, 260 a karshen makon nan. Daga cikin masu kammala karatun akwai har Dalibai akalla 256 da su zama Dakta.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel