Nigerian news All categories All tags
Ana zargin Maryam Sanda da kashe Mijin ta saboda bakin kishi

Ana zargin Maryam Sanda da kashe Mijin ta saboda bakin kishi

- Ana zargin Maryam da kashe Mijin ta don tsabar bakin kishi

- Yanzu haka Bilyaminu ‘Dan gidan Halliru Bello ya bar Duniya

- Maryam Sanda kuma ta shiga Kotu da casbaha da Al-Kur’ani

Kwanaki aka samu wata Baiwar Allah da ake zargi ta hallaka mijin ta har lahira saboda tsabar kishi. Yanzu haka dai ana cigaba da shari’a a Birnin Tarayya Abuja domin gane gaskiyar lamarin.

Ana zargin Maryam Sanda da kashe Mijin ta saboda bakin kishi

Za ka auri Maryam Sanda idan har ta tuba ga Allah?

Maryam Sanda yanzu haka tana Kotu kuma ta karyata cewa ita ta kashe mijin ta Bilyaminu Halliru Bello da hannun ta. Wasu dai sun a ganin tana da gaskiya, wasu kuma na ganin shari’ar sai a lahira yayin da wasu ma ke cewa tayi daidai.

KU KARANTA: Wani yayi wa Diyar sa fyade a Garin Legas

Akwai rade-radin kishi ne ya sa Maryam ta sa tsohon Mijin na ta ya rabu da matar sa don ya aure ta kuma ta hana shi ya kara neman aure. Ko ma dai ya ake ciki yanzu haka Jama’a na ta ce-ce-ku-ce game da lamarin da ya faru kwanaki.

Wani Bawan Allah kwanaki yace shi fa a shirya yake da ya aure ta idan ya samu hali. Bayan nan dai an ta samun labaran cewa wata ta hallaka mijin ta ko yaran sa ko kuma tayi yunkurin haka. An dai ga Maryam a Kotu da Kur’ani tana karatu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel