Nigerian news All categories All tags
Rikici kan budurwa ya tunzura wasu dalibai 3 sun kashe wani Mutum a Katsina

Rikici kan budurwa ya tunzura wasu dalibai 3 sun kashe wani Mutum a Katsina

- Jami'an rundunar yan sandan Jihar Katsina sun cafke wasu dalibai 3

- Kwamishinan yan sanda na Jihar, Benson Gwana ya bayyanawa wa manema labarai ana zargin su da aikata kisan kai

- An cafke daliban ne bayan sunyi wa mammacin rauni masu tsanani a dalilin wata budurwa da suke nema

Jami'an rundunar yan sandan Jihar Katsina sun cafke wasu dalibai 3 da ke karatu a Jami'ar Umaru Musa Yaradua da ke Katsina bisa laifin kashe wani bawan Allah mai sunanAbdulmalik Kabir kan wata mace da suke nema.

Rikici kan budurwa ya tunzura wasu dalibai 3 sun kashe wani Mutum a Katsina

Rikici kan budurwa ya tunzura wasu dalibai 3 sun kashe wani Mutum a Katsina

Kamar yadda Kwamishinan yan sanda na Jihar, Benson Gwana ya bayyanawa wa manema labarai a ranar Juma'a, daliban da ake zargi da aikata kisan kai duka maza ne, guda 2 na aji 3, shi kuma guda yana aji 2 duk dai a Jami'ar.

DUBA WANNAN: Dalilin da yasa yin wasan Hausa da yaren turanci keda muhimanci - jaruma Fati SU

Jami'an yan sanda sun cafke daliban ne bayan sunyi wa mammacin rauni masu tsanani a dalilin wata budurwa da suke nema.

An garzaya da mammacin asibiti inda yake karaban magani amma daga baya ya rasu a cikin watan Nuwamba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel