Nigerian news All categories All tags
Shugaba Buhari bai damu da samun tikitin takara kyauta ba - Tsohon Gwamna

Shugaba Buhari bai damu da samun tikitin takara kyauta ba - Tsohon Gwamna

Tsohon gwamnan jihar Abia, Orji Uzor Kalu, ya ce ba damuwar shugaba Buhari ba ne samun kyautar tikitin yin takara na jam'iyyar APC ba a zaben shugaban kasa na shekarar 2019.

Kalu ya fadi hakan ne a yau Asabar a filin jirgin sama na Murtala Muhammed dake jihar Legas.

Ya ce "shugaba Buhari mutum ne mai adalci da kamanta gaskiya, a saboda haka ba zai hana duk mai sha'awar tsayawa takara karawa da shi ba, shi kan sa shugaba ya bayyana cewar ba adalci ba ne a hana kowa tsayawa takara ba matukar yana da sha'awar hakan".

Tsohon Gwamna Uzor Kalu

Shugaba Buhari bai damu da samun tikitin takara kyauta ba - Tsohon Gwamna

Tsohon gwamnan ya bayyana cewar zai bawa shugaba Buhari goyon baya matukar zai kara tsayawa a zaben shekarar 2019.

DUBA WANNAN: Wani dan sanda ya kira ruwa bayan ya kwaci N40,000 a hannun wani da ya kama

Kalu ya ce aiyukan da shugaba Buhari ya yi a kasa sun isa su zamar ma sa hujjar samun goyon bayan 'yan Najeriya domin ko a halin yanzu yana kuri'ar maboya baya mutum miliyan 15 duk da rashin lafiyar da ya hana shi zama na tsawon lokaci.

Kalu ya ce jam'iyyar PDP ba zata iya karbar mulki a zaben na 2019 tare da kara nanata cewar shugaba Buhari ya cancanci kara tsayawa neman kujerar shugabancin Najeriya karo na biyu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel