Nigerian news All categories All tags
Yan sanda sun ceto Mai Unguwa da wasu mutane 3 daga hannun masu garkuwa da mutane

Yan sanda sun ceto Mai Unguwa da wasu mutane 3 daga hannun masu garkuwa da mutane

Rundunar yan sanda reshen Jihar Neja tayi nasarar ceto wani mai unguwan kauyen Unguwar gizo da ke karamar hukumar kagara da wasu mutane 3 daga hannun masu garkuwa da mutane.

Masu garkuwa da mutanen sun sace mai Unguwan da sauran mutanen tun ranar 21 ga watan Nuwamba a garin su na Unguwar Gizo da ke karamar hukumar ta Kagara.

Yan sanda sun ceto Mai Unguwa da wasu mutane 3 daga hannun masu garkuwa da mutane

Yan sanda sun ceto Mai Unguwa da wasu mutane 3 daga hannun masu garkuwa da mutane

Kwamishinan rundunar yan sanda na Jihar Austine Agbonlahor ne ya bayyanawa kamfanin dillancin labarai NAN cewa rundunar tayi nasarar ceto su ne yayin wata samame da suka kai tare da hadin gwiwar wasu yan kungiyar Banga daga garin Birnin Gwari da ke Jihar Kaduna.

DUBA WANNAN: Ku shigo APC, ku samu mukamai a Gwamnatin Tarayya, Oshiomhole ya fadawa al'ummar Isoko

Ya kara da cewa rundunar tana kara daukan matakan da suka dace domin tabbatar da tsaron lafiya da dukiyoyin al'umma. Ya cigaba da cewa rundunar zata tura Jami'an ta baza jami'an ta a duk wuraren da ake tsamanin bata garin suna gudanar da ayyukansu.

Yayi kira da al'umma su cigaba da baiwa rundunar hadin kai ta hanyoyin bada bayyanai masu amfani domin kara tabbatar da tsaro.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel