Nigerian news All categories All tags
Gwamnati na adana wa Najeriya Naira biliyan 25 duk wata - Shugaba Buhari

Gwamnati na adana wa Najeriya Naira biliyan 25 duk wata - Shugaba Buhari

- Ya ce shirin gwamnati na ciyarwa a makarantun firamare zai cigaba

- Gwamnati ta toshe hanyoyin zurarewar kudi

- Babu gudu babu ja da baya a yaki da cin hanci

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewar gwamnatin sa na adana wa Najeriya Naira biliyan 25 wata ta hanyar dakatar biyan alawus marasa dalili ga ma'aikata da kume toshe hanyoyin zurarewar kudi.

Gwamnati na adana wa Najeriya Naira biliyan 25 duk wata - Shugaba Buhari

Osinbajo

Shugaban ya yi wannan magana ne a yau Asabar ta bakin mataimakin sa, Farfesa Yemi Osinbajo, yayin da ya wakilce shi a bikin yaye wasu da suka kamma karbar horo a makarantar bayar da horo ga maikata, NIPSS, daku Kuru a jihar Filato.

DUBA WANNAN: Wani dan sanda ya kira ruwa bayan ya kwaci N40,000 a hannun wani da ya kama

Ya bayyana cewar gwamnatin su ba zata saurara a yakin da take da cin hanci ba tare da yin albishir ga 'yan Najeriya cewar matsalar wutar lantarki kwanannan zata zama tarihi.

Jami'an tsaro ne suka fi yawa cikin wadanda suka kammala karbar horon da adadin mutum 28 cikin 66 cikin su harda wata mace kwamishinar 'yan sanda.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel