Nigerian news All categories All tags
An yi kicibis da gawar wani dan aji uku a jami'ar ATBU rataye a jikin bishiya

An yi kicibis da gawar wani dan aji uku a jami'ar ATBU rataye a jikin bishiya

- Ba'a san dalin da ya sa ya kashe kan sa ba

- Rahoto ya zo cewa an kwantar da shi a asibitin koyarwa kwana biyu kafin mutuwar sa

- 'Yan sanda sun bude shafin bincike

Mutane sun ci karo da gawar wani dalibin jami'ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBU) da ke Bauchi rataye a jikin bishiya, wanda ake kyautata zaton shi ya rataye kan shi a jiya Juma'a.

Gawar Dahiru Adamu a rataye jikin bishiya

Gawar Dahiru Adamu a rataye jikin bishiya Hoto daga: Information Nigeria

Hotunan dalibin dan aji uku a jami'ar mai suna Dahiru Adamu dan shekara 30, sun zaga kafofin sada zumunta na yanar gizo. Dalibin yana karantar kafinta a jami'ar.

Wannan abu ya auku ne a harabar jami'ar ta Gubi, da ke kan Titin Kano.

Wani dalibi ya baiyanawa manema labarai cewa an bar gawar ta fi awa biyu a rataye.

"A yanzu haka na ga shugaban makarantar da motar agaji a wajen. Ina kyautata tsammanin suna jiran 'yan sanda ne su karaso.

Hukumar jami'ar yayin da suke jiran zuwan 'yan sanda

Hukumar jami'ar yayin da suke jiran zuwan 'yan sanda Hoto daga: Information Nigeria

"Marigayin ya bar takalman sa da littattafan sa a karkashin bishiyar kafin ya rataye kan shi.

"Ban san marigayin ba amma na ji an ce sunan shi Dahiru, dan aji uku. Ya kamata ace yanzu yana wajen koyan aikin dalibai (SIWES) amma bai tafi ba a bana."

Mai magana da yawun bakin 'yan sandar jihar Bauchi, Kamal Datti, ya gaskata wannan lamari. Yace shugaban tsaron makarantar ne ya kira su ya sanar da su.

"Mun sauko da gawar sannan muka mika ta zuwa mutuwaren asibitin koyarwa na jami'ar. Kuma mun samu rahoton cewa a ranar Larabar da ta gabata an kwantar da marigayin a asibitin amma an sallame bayan ya samu sauki a ranar."

DUBA WANNAN: Wani dan sanda ya kira ruwa bayan ya kwaci N40,000 a hannun wani da ya kama

Datti ya gama da cewa ba su da tabbacin me ya janyo mutuwar wannan dalibi, amma sun bude bincike don su gano diddigin lamarin.

"A yanzu haka muna cigiyar iyalan sa don mu sanar da su abin da ya auku."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, a tuntube mu a:

labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel