Nigerian news All categories All tags
Wani dan sanda ya kira ruwa bayan ya kwaci N40,000 a hannun wani da ya kama

Wani dan sanda ya kira ruwa bayan ya kwaci N40,000 a hannun wani da ya kama

- Mutumin ya ce an kamashi ba gaira ba dalili

- Ya samu ya dauki hoton wanda ya bada lambobin asusun da ya tura kudin, a yanzu haka an kama dan sandan

- Hukumar korafi ta sha alwashin bin diddigin lamarin

Hukumar karbar korafin al'umma (PCRRU) ta bude shafin bincike bayan ya baiyana a kafofin sada zumunta na yanar gizo cewa wani dan sanda ya kwacewa wani mai suna Dapo N40,000 bayan an kama an kai shi caji-ofis.

Dapo, wanda ba'a baiyana cikakken sunan sa ba, ya ce wasu 'yan sanda sun zo sun kama shi sun tafi da shi ofishin su na Maroko, a Legas. Daga bisani sai suka yi ta gallaza masa da duka har sai da suka sa ya aika musu da kudi N40,000 ta banki.

Aiken kudin da Dapo ya yiwa dan sandan

Aiken kudin da Dapo ya yiwa dan sandan

Dapo a rubuta, "Ban san me nayi ba. Muna zaune da abokai na a cikin motar su a Lekki da misalin 1.30 na dare, sai suka zagaye mu suka ce mu sauko daga motar. Suka bincike mu ba su sami komai ba. Kawai sai suka sa min ankwa suka tasa keya ta zuwa ofishin su na Maroko. Nan sukai ta gallaza min da duka sannan suka sa ni na aika da kudin zuwa wani asusun kafin suka sake ni. Dan sandan da ke cikin hoton nan shine ya bani lambar asusun mai dauke da sunan Bamodu B. Oluwatoyin da na aika kudin."

PCRRU sun sa wa binciken labar #PCCRU600772. Binciken farko ya nuna cewa sun sami gaskiyar cewa tabbas an kama wannan mutumi an kai shi caji-ofis na Maroko. Sannan kuma dan sandan dake cikin hoton shine mataimakin Sufritenda na 'yan sandan, wanda ba su baiyana sunan shi ba. Amma sun ce sunan da ke kan asusun da aka tura kudin ba sunan dan sandan bane. Saboda haka a yanzu suna nan suna binciken wanene me asusun bankin.

A yanzu haka PCRRU ta kama wannan sufritendan dan sanda ta mika shi hannun X-Squad na jihar kamar yadda shugaban 'yan sandar jihar, Ag. CP Inohimi Edgal, ya bada umarni.

PCCRU na kira ga Dapo da in ya ga wannan ya neme su don ya basu cikakken bayani don a samu a fito masa da hakkin sa.

DUBA WANNAN: Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan Kodin a cikin matasa

Sun kuma baiyana cewa duk dan sandan da ya sake ya shiga hannun su saboda karbar cin hanci ko kwacen kudi, sai inda karfin ta ya kare don gurfanar da shi a gaban sharia.

Sun gama da cewa yin beli kyauta ne. Kar wanda ya yadda ya biya 'yan sanda kudi saboda yin beli.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, a tuntube mu a:

labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel