Nigerian news All categories All tags
Wani mahaifi ya fyade 'yar sa mai shekaru 12 a jihar Legas

Wani mahaifi ya fyade 'yar sa mai shekaru 12 a jihar Legas

Wani mahaifi mai shekaru 35 ya gurfana a gaban kotun majistire ta Ogudu dake jihar Legas a ranar Jumma'ar da ta gabata, bisa laifin lalata da 'yar sa ta cikin sa mai shekaru 12 a duniya.

Wannan mahaifi Idoko, kamar yadda jami'in dan sanda mai shigar da kara a gaban kotun, Sajen Lucky Ihehie ya shaida, mahaifin yarinyar ya fyade ta ne a gidan su mai lamba 35 na layin Akinwonsola dake unguwar Oworonshoki ta gundumar Kosofe a jihar ta Legas.

Idoko a halin yanzu zai fuskanci fushin kotu bisa aikata laifin da ya sabawa dokar jihar Legas ta karkashin sashe na 137, 160 da kuma 170.

Kamar yadda shugaban kungiyar kare hakkin bil Adama Misis Titilola Vivour-Adeniyi ta bayyana, wannan rashin tunani na fyade 'yar sa da mahaifin yayi ya fara ne tun a watan Yulin shekarar 2017.

Wannan abu dai ya faru ne a gidan su mai daki daya inda mahaifin ya zakkewa 'yar ta sa, wanda bincike ya bayyana cewa, sun rabu da mahaifiyar ta tun shekaru uku da suka gabata, inda Idoko ya hana matar ta sa tafiya da 'ya'yan su.

Wani mahaifi ya fyade 'yar sa mai shekaru 12 a jihar Legas

Wani mahaifi ya fyade 'yar sa mai shekaru 12 a jihar Legas

Mahaifin su na rayuwa a wannan gida mai daki guda tare da 'ya'yayen sa mata biyu, 'yan shekaru 12 da 9. Yarinyar da abin ya shafa ta tunano tun a watan Yulin da ya gabata, inda mahaifin na ta yayi mata bintir da misalin karfe 11:00 na dare kuma ya aikata alfashar da ita ba tare da amincewar ta ba.

Ta ke cewa, tun daga wannan lokaci mahaifin na ta ya cigaba da biyan bukatar sa da ita mako bayan mako, musamman ma a daren ranakun Talata da Laraba.

Wannan lamari ya sanya yarinyar dake aji na biyar a makarantar Firamare ta susuce, inda ta labartawa wata 'yar jarida halin da ta ke ciki bayan ta tursasa akan sai ta bayyana mata damuwar ta.

KARANTA KUMA: Shugaba Buhari ya jajinta akan harin masallaci da ya salwantar da akalla rayuka 270 a kasar Masar

Cikin gaggawa 'yar jaridar ta shigar da rahoto ofishin 'yan sanda, kuma nan da aka garzaya asibiti da yarinyar kuma aka tabbatar ta wannan abin tausayi da ya sha afkuwa akan ta.

Tuni dai mahaifin wannan yarinya ya gurfana a gaban kotu, inda alkaliyar kotun ta bayar da belin shi akan kudi Naira 200, 000 tare da bayar da mutane biyu da zasu tsaya masa a matsayin jingina, ta kuma daga sauraron karar zuwa ranar 12 ga watan Dasumba domin yanke masa hukunci.

Legit.ng ta fahimci cewa, irin wannan laifi ya kan fuskanci hukunci dauri a gidan kaso har na tsawon shekaru 14 kamar yadda dokar kasa karkashin sashe na 137 ya tanadar.

LATSA WANNAN: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel