Nigerian news All categories All tags
Hukumar EFCC ta kama kadarori 3 na tsohon gwamnan jihar Benue

Hukumar EFCC ta kama kadarori 3 na tsohon gwamnan jihar Benue

Legit.ng ta samu rahoton cewa, hukumar EFCC ta dira akan tsohon gwamnan jihar Benue Gabriel Suswam, inda ta kame kadarori har uku wanda mallakin tsohon gwamnan ne.

Shafin jaridar PoliticsNGR ta ruwaito cewa, tuni hukumar ta datse gidajen tsohon gwamnan inda ta yi rubuce-rubucen da ta saba da jan fenti, na alamar hukumar tana gudanar da bincike akan gidajen saboda haka a yi hattara.

Tsohon gwamnan jihar Benue Gabriel Suswam

Tsohon gwamnan jihar Benue Gabriel Suswam

Kadarorin da hukumar ta datse sun hadar da; wani gidan wanda ba a ko karasa ginin shi ba, gidan su na gado dake unguwar HUDCO sai kuma Otel din sa na Metropolitan dake kan hanyar cibiyar lafiya ta gwamnatin tarayya wato FMC (Federal Medical Centre) dake birnin Makurdi.

KARANTA KUMA: Falae ya caccaki gwamnatin shugaba Buhari

An yi rashin sa'ar ganawa da lauyan kolu na jihar Musa Gida a yayin tuntubarsa, domin jin ta bakin sa akan badakar tsohon gwamna Suswam.

Hukumar ta EFCC tana bincikar tsohon gwamnan akan almundahanar Naira Biliyan 107 da yayi a lokacin da yake gwamnan jihar ta Benue.

LATSA WANNAN: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel