Nigerian news All categories All tags
Falae ya caccaki gwamnatin shugaba Buhari

Falae ya caccaki gwamnatin shugaba Buhari

Tsohon ministan kudi kuma tsohon manemin shugabancin Kasar Najeriya, Cif Olu Falae, ya caccaki gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari, inda ya ce kokarin Buhari a kan kujerar mulki har yanzu bai taka kara ya karya ba.

Falae ya bayyana cewa, babu wani tasiri da gwamnatin Buhari ta yi tare da bayar da tabbataci akan fita da matsin tattalin arziki ba wani abu bane face yaudara.

A yayin ganawa da manema labarai na jaridar Sun, dattijon na Najeriya ya nemi shugaba Buhari da ya kara zage dantsen sa da kyau a madadin batu da yake na cewar bai tarar da komai ba a asusun gwamnati.

Tsohon Ministan Kudi Olu Falae

Tsohon Ministan Kudi Olu Falae

Falae yake cewa, "idan ya duba jihar sa ta Ondo kuma ya kalli yadda hanyoyi suka lalace. Sai ya ga babu wani abu da gwamnatin Buhari take yi, kuma zance an fita daga matsin tattalin arziki har yanzu batu na shaci fadi, domin mutumin da yake kan titi bai ji danshin hakan ba."

KARANTA KUMA: Shugaba Buhari ya jajinta akan harin masallaci da ya salwantar da akalla rayuka 270 a kasar Masar

"Sauyin da aka samu na farashin man fetur ya kamata a ce samun mutane ya karu. Idan aka gyara wutar lantarki adadin mutane da su koma aiki ba kadan bane, sakamakon dubunnan masana'antu da zasu mike tsaye."

Falae ya ke cewa, "gwamnatin Buhari ba za musaltu da ta tsohon shugaba na mulkin soja, Ibrahim Badamasi Babangida, domin kuwa a lokaci farashin man fetur bai taka kara ya karya ba, amma gwamnatin tayi fice da zamtowa abar alfahari sakamakon manyan ayyuka da ta gudanar."

LATSA WANNAN: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel