Nigerian news All categories All tags
Mutane 4 da ka iya bin sahun Atiku bayan ficewar sa daga APC

Mutane 4 da ka iya bin sahun Atiku bayan ficewar sa daga APC

Ficewar tsohon mataikamkin shugaban kasa Atiku Abubakar daga jam'iyyar APC bai baiwa masu nazarin siyasa mamaki ba, musaman idan akayi la'akari da cewa Turakin Adamawan bai boye rashin jin dadinsa ga yadda aka maida shi saniyan ware ba bayan gudunmwar da ya bada wajen samun nasara a zaben 2015.

Al'addar yan siyasa ne sakawa wadanda suka taimaka wajen nasarar zabe da mukamai ko kwangila amma idan aka lura, Atiku Abubakar baida wasu mutane nashi a cikin gwamnatin ila Ministan Harkokin Mata, Aisha Al-Hassan da kuma babban mataimakin shugaban kasa na musamman a fanin kafafen yadda labari, Garba Shehu wanda bazai zama abin mamaki ba idan suka bi sahun turakin Adamawan, amma bayan su, su wanene ka iya bin Atikun?

1) Garba Shehu

Mutane 4 da ka iya bin sahun Atiku bayan ficewar sa daga APC

Mutane 4 da ka iya bin sahun Atiku bayan ficewar sa daga APC

Kafin nadin sa a matsayin mai mataimakin shugaban kasa a fanin kafafen yadda labarai, Shehu yayi aiki a matsayin mataimakin Atiku na fanin kafafen yadda labari tun shekarar 2003 kamar yadda ya bayyana a wata hira da yayi.

Idan akayi la'akari da yadda tsawon shekarun da Shehu yayi aiki karkashin Atiku da kuma yadda yake mutunta tsohon shugaban nasa, ba abin mamaki bane ya bi shi duk inda ya tafi musamman tunda ainihi Buhari ya so Femi Adesina ne a matsayin hadimin nasa.

KU KARANTA: Na kashe jaririn kishiya na bisa kuskure ne, Inji Rabi'atu

2) Aisha Al-Hassan

Mutane 4 da ka iya bin sahun Atiku bayan ficewar sa daga APC

Mutane 4 da ka iya bin sahun Atiku bayan ficewar sa daga APC

Ministar harkokin mata Aisha Al-Hassan wadda akafi sani da Mama Taraba bata taba boye biyayar ta Atiku Abubakar ba wanda tace shine maigidanta tun kafin ta zama Minista.

Idan masu karatu basu manta ba, kwanakin baya ta bayyanawa duniya cewa ko da Buhari zai tsaya takara ita Atiku zata zaba duk da cewa tana aiki karkashin gwamnatin Buhari.

3) Bukola Saraki

Mutane 4 da ka iya bin sahun Atiku bayan ficewar sa daga APC

Mutane 4 da ka iya bin sahun Atiku bayan ficewar sa daga APC

Al'umma da dama suna zargin cewa Bukola Saraki baya tare da gwamnatin Buhari musamman idan aka duba baddakalar da akayi kafin ya zama Shugaban Majalisa da kuma yadda ya rika kaiwa Atiku ziyara bayan ya zama shugaban Majalisar.

Mutane da dama suna ganin abotan su da ta samo asali tun a jam'iyyar PDP tana nan daram kuma ba zaiyi wata-wata ba wajen sauya sheka idan bukatan hakan ta taso tunda ba wannan ne zai zama karo na farko ba.

4) Yakubu Dogara

Mutane 4 da ka iya bin sahun Atiku bayan ficewar sa daga APC

Mutane 4 da ka iya bin sahun Atiku bayan ficewar sa daga APC

Kamar Saraki, Mutane da dama suna ma Yakubu Dogara kallon mutanen da suka dawo APC ba da niyyar ganin cigaban jam'iyyar ba sai dai kawai domin biyan wata bukata tasu.

Duk da cewa ya sauya sheka zuwa APC, mutane da dama suna masa kallon angulu da kan zabo, kuma kamar Aisha Al-Hassan shima Atiku mai gida ne a wurin sa kuma akwai yiwuwar ya zai iya ficewa daga APC domin yabi sahun Atiku Abubakar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel