Nigerian news All categories All tags
Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan Kodin a cikin matasa

Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan Kodin a cikin matasa

- An yi taron shekara-shekara na kungiyar kula da lafiyar mata ta SOGON a Sakkwato

- Sarakuna da gwamnoni sun sami halarta

- Kowa ya baiyana irin gyaran tsarin lafiyar da yake bayarwa mata da yara a jihar sa

Sarkin Musulmi, Sultan Sa'ad Abubakar III, ya koka da yadda matasa suka dunguma suna shan maganin murar nan Kodin. Ya yi kira ga jami'ai da su kawo dauki don rage hanyoyin da kowa zai iya samun maganin.

Abubakar yayi wannnan magana ne a ranar Juma'a a Sakkwato, yayin da ake yin taron shekara-shekara na 51 na kungiyar kula da lafiyar mata (SOGON), wanda ya dau taken "Daular Musulunci a 2017."

Sarkin Musulmi Sultan Abubakar

Sarkin Musulmi Sultan Abubakar

Sarkin Musulmi ya yaba da wannan taron kuma yayi kira ga wadanda suka halarta da su zage dantse don neman lafiyar mata don a rage mutuwa. Kuma ya ce zai tilastawa sarakunan da ke kasan shi da su dauki hanyoyin kula da lafiyar mata a cikin al'umman su.

Taron ya sami halartar sarakuna, 'yan siyasa, gwamnoni, da mukarraban gwamnati.

Gwamnan jihar Sakkwato Aminu Tambuwal, wanda yana daa cikin gwamnonin da suka halarci taron, ya ce gwamnatin shi ta kaddamar da inshorar lafiya don bunkasa lafiyar mata da yara, da kuma yiwa yara rigakafi kyauta, da kuma nema musu lafiya a kan cututtuka irin su maleriya da sauran su.

Ya kara da cewa a yanzu haka suna shirin kaddamar da aikin sabon asibitin koyarwa na jami'ar jihar, sannan kuma suna gyara kwalejin koyan aikin nas da ungozomanci, da sauran makarantu da ma'aikatun neman lafiya.

Ya jinjina wa SOGON da suka karrama gwamnan jihar Yobe Ibrahim Geidam, wanda shima ya halarci taron. SOGON ta ba Geidama karramawar zama memban ta.

Geidam ya ce wannan karramawar karin karfin gwiwa ne don ya ci gaba da fafutikar gyaran samun lafiya a jihar sa.

Ya ce zai yi kokarin samar da lafiya kyauta ga mata masu ciki da masu shayarwa da kuma wadanda suka samu hatsari. Ya kuma ci alwashin gyaran asibitoci da siyo sababbin injinan binciken lafiya.

DUBA WANNAN: Kana kin naka wani na so: Burundi na neman Najeriya ta ara mata tsarin ilimin ta

Geidam ya baiyana cewa a yanzu haka gwamnatin shi har ta bude sabon asibitin koyarwa na jami'ar Yobe mai dauke da gadajen marasa lafiya 250, sannan kuma gwamnatin shi ta dau nauyin karatun likitanci na dalibai har 600, kuma ana basu albashi.

A taron, SOGON ta karrama mutane 39 da zama membobin su. Da aka gama kuma, shugaban asibitin koyarwa na jami'ar Usmanu Danfodio (UDUTH), ya sanar da mutane cewa SOGON ta bude wani fagen bada lafiya da tiyata kyauta a asibitin na dan wani lokaci don wannan taron da aka gudanar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, a tuntube mu a:

labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel