Kana kin naka wani na so: Burundi na neman Najeriya ta ara mata tsarin ilimin ta

Kana kin naka wani na so: Burundi na neman Najeriya ta ara mata tsarin ilimin ta

- Wakilin Burundi ya kai wa ministan ilimi ziyara a Abuja

- Ya nemi a ara musu takardun tsarin ilimi

- Ministan ilimi ya yi murna, ya tula masa su

Jamhuriyar Burundi ta kai rokon ta ga gwamnatin tarayyar Najeriya don a bata izinin aron tsarin ilimin da Najeriya take amfani da shi a makarantu.

Wakilin Burundi na Najeriya, Mista Emmanuel Mpfayakurera, ne ya yi wannan rokon a Abuja yayin da ya kai wa ministan ilimi Mallam Adamu Adamu ziyarar sada zumunta a ranar juma'a.

Minisan Ilimi na kasa Mallam Adamu Adamu da Wakilin Burundi na Najeriya Mista Emmanuel Mpfayakurera

Minisan Ilimi na kasa Mallam Adamu Adamu da Wakilin Burundi na Najeriya Mista Emmanuel Mpfayakurera

Mpfayakurera ya ce, "Muna neman ku yarje wa kasar mu yin amfani da tsarin ilimin da kuke amfani da shi a nan, har da yadda kuke horar da masu bada ilimin (TVET)."

Wakilin ya kuma yiwa Najeriya godiya a kan taimakon da ta kai wa kasar sa lokacin da rikici ya barke.

Adamu Adamu ya amsawa Mpfayakurera cewa Najeriya a shirye take don ta kara karfin zumunci da Jamhuriyyar Burundi musamman ma ta harkar ilimi.

DUBA WANNAN: 'Yan sanda sun gano wasu 'yan ci rani a boye cikin tankar mai

"A shire muke mu baku wannan tsarin ilimin don kuma ku yi amfani da shi."

Adamu Adamu ya sa an debo littattafai da takardu da dama na tsarin ilimin Najeriya an bawa wakilin Burundin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, a tuntube mu a:

labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel