Batan-baka-tan-tan: Jam'iyyar PDP ta sarewa Atiku gwuiwa game da batun takarar sa a 2019

Batan-baka-tan-tan: Jam'iyyar PDP ta sarewa Atiku gwuiwa game da batun takarar sa a 2019

Babbar jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya ta yi tsokaci a game da batun ficewa daga jam'iyyar APC da tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya kuma fitaccen dan siyasa, Alhaji Atiku Abubakar inda ta bayyana shi a matsayin wani mai 'yanci a yanzu.

Sai dai kuma jam'iyyar a cikin wani zance mai kama da na sare gwiwa, ta bayyana cewa tikitin ta na takara a zaben 2019 mai zuwa ba na kowa bane don haka ba zai same shi ba hakanan kai tsaye sai yayi takarar neman sa.

Batan-baka-tan-tan: Jam'iyyar PDP ta sarewa Atiku gwuiwa game da batun takarar sa a 2019

Batan-baka-tan-tan: Jam'iyyar PDP ta sarewa Atiku gwuiwa game da batun takarar sa a 2019

KU KARANTA: Zamfara ta samu sabon kwamishinan 'yan sanda

Legit.ng dai ta samu cewa a cikin sanarwar da jam'iyyar ta PDP ta fitar, ta bayyana cewa hakika Allah ne ya nufi tsohon mataimakin shugaban kasar da shiriya shine babban dalilin da yasa ya fita yabar jam'iyyar.

Daga nan ne kuma sai jam'iyyar ta mika sakon gayyata ga duk wanda yake ganin ba'a yi masa adalci a jam'iyyar ta APC da ya garzayo a jam'iyyar tasu domin su jam'iyyar su jam'iyya ce mai adalci ga kowa.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel