Nigerian news All categories All tags
Mutum guda ya shiga hannu da laifin kisan Sakataren jam'iyyar APC

Mutum guda ya shiga hannu da laifin kisan Sakataren jam'iyyar APC

Kwamishinan 'yan sandan jihar Katsina, Besen Gwamna, ya bayar da sanarwa da take tabbatar da mutuwar sakataren jam'iyyar APC, Idris Nature, na karamar hukumar Dutsinma.

Kwamshinan na 'yan sanda ya bayar da sanarwar ne yayin ganawa da manema labarai a birnin jihar inda ya bayyana cewa, an gano gawar mamacin tare da raunuka da dama a kan sa.

Gwamna ya bayyana cewa, wani Aliyu Bala mai inkiyar Ubangaja, ya shiga hannu bisa zargin sa da ake na sa hannu kisan jigon na APC.

Mutum guda ya shiga hannu da laifin kisan Sakataren jam'iyyar APC

Mutum guda ya shiga hannu da laifin kisan Sakataren jam'iyyar APC

A kalaman sa, "da misalin karfe 8:30 na daren ranar 19 ga watan Nuwamba, wani Aliyu Bala mai inkiyar Ubagaja dan shekaru 54, ya bukaci marigayi Idris da ya raka shi zuwa kauyen Kuki dake karkashin karamar hukumar Dutsinma a jihar Katsina."

KARANTA KUMA: Buhari ya karkata kan mafi karancin albashin ma'aikatan Najeriya

"A yayin haka ne a kashe garin ranar 20 ga watan Nuwamba da misalin karfe 7:00 na sfiya, aka tsinto gawar marigayi Idris kwance akan hanyar kauyen na Kuki da raunuka a kan sa.

"Sai kuwa jami'an 'yan sanda suka bi sawun baburin marigayin har gidan wanda ake zargi Ubangaja, kuma suka yi ram da shi, wanda a yanzu bincike ya kan kama domin gano gaskiyar lamarin."

LATSA WANNAN: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel