Nigerian news All categories All tags
Fasinjoji 19 sun ƙone ƙurmus a wani hatsarin jihar Imo

Fasinjoji 19 sun ƙone ƙurmus a wani hatsarin jihar Imo

Fasinjoji 19 sun riga mu gidan gaskiya yayin da suka ƙone ƙurmus sakamakon wuta da ta kama wata motar haya mai cin mutane 18 akan hanyar ta daga garin Orlu zuwa birnin Owerri na jihar Imo, inda ta hadu da wata tankar mai a ranar Jumma'ar da ta gabata.

Legit.ng ta ruwaito da sanadin jaridar Punch cewa, tankar ta mai ta dauko makamashin gas ne wato Diesel akan hanyar zuwa Orlu yayin da wannan hatsari ya afku a gadar Jaba a babbar hanyar ta birnin Owerri.

Jami'an 'yan sanda ta bayar da tabbacin fasinjoji 17 daga cikin wanna mota sun sheka da kuma wasu fasinjoji 2 dake cikin tankar ta mai, inda wata mace guda daje cikin motar hayar ta tsallake rijiya da baya.

Fasinjoji 19 sun ƙone ƙurmus a wani hatsarin jihar Imo

Fasinjoji 19 sun ƙone ƙurmus a wani hatsarin jihar Imo

Wani mashaidin wannan lamari ya labartawa manema labarai cewa, hatsarin ya afku ne yayin da motoci biyu suka gwabza da juna kuma nan da nan wuta ta kama, inda wutar ta datse fasinjojin a ciki.

KARANTA KUMA: Buhari ya karkata kan mafi karancin albashin ma'aikatan Najeriya

A yayin da aka kashe wannan wuta da ta kama, fasinjojin sun ƙone ƙurmus ta yadda ba a iya gane su. Wannan ibtila'i da ya afku ya janyo zulumi cikin al'ummomi da matafiya da dama da suka tsaya agaji tare da ma'aikatan hukumar manyan hanyoyi ta FRSC

Kakakin hukumar 'yan sanda Andrew Enwerem, ya bayar da tabbacin mutuwar fasinjoji 19, inda shugaban hukumar FRSC reshen jihar Kayode Aremu, ya bayar da sanarwar a wata ganawa da manema labarai na gidan talabijin din jihar.

LATSA WANNAN: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel