Nigerian news All categories All tags
Gwamnatin Kano na kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata – Inji Ganduje

Gwamnatin Kano na kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata – Inji Ganduje

- Gwamna Ganduje ya koka game da naira biliyan 9 da gwamnatinsa ke kashewa a kowane wata

- Gwamnan ya ce jihar ba ta kasa biya albashi na kowane wata ba

- Ganduje ya bayyana cewa shirin “Mai Shai Empowerment Scheme”, ya inganta rayuwar mutane da dama a jihar

Gwamnatin jihar Kano ta bayyana cewa tana kashe naira biliyan 9 a kowace wata wajen biyan albashin ma’aikatan jihar.

Gwamna Abdullahi Ganduje ya fada hakan ne a Kano a ranar Juma'a, 24 ga watan Nuwamba a rana ta biyu a taron NDIC wanda aka shirya wa 'yan jaridun kudi.

Ya ce duk da cewa gwamnati na biyan albashi mai yawa, wanda ya ce, ta fi fiye da jihohi 3 idan aka hada, ya ce jihar ba ta kasa biya albashi na kowane wata ba.

Gwamnatin Kano na kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata – Inji Ganduje

Gwamnatin Kano na kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata – Inji Ganduje

Gwamnan, wanda sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Rabiu Bichi ya wakilta, ya ce, jihar ta fara aiwatar da shirye-shiryen karfafawa don inganta rayuwar mazauna.

KU KARANTA: Sarkin Kano ya zargi su babba da jaka bisa halin tabarbarewar arzikin Najeriya

Ya bayyana daya daga cikin shirye-shiryen watau shirin “Mai Shai Empowerment Scheme”, wanda aka shirya wa masu sayar da shayi a jihar.

Ganduje ya ce wannan shirin ya inganta rayuwar mutane da dama a jihar.

Kamar yadda Legit.ng ke da labari , gwamnan ya bayyana cewa, za a farfado da masana'antar buga yadi da ke Kano, wanda ita ne ta kasance masana'anta mafi girma a Afirka.

Ganduje ya ce, masu zuba jarurruka na kasashen waje sun ziyarci jihar tare da neman zuba jarurruka a wasu daga cikin wadanan masana'antu.

Ya ce jihar tana da mafi yawan yara masu shiga makarantun firamare a Najeriya na fiye da miliyan 3 da jami'o'i 2 a jihar.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel