Tsugune-bata-kare-ba: Jam'iyyar PDP na shirin sake darewa gida 2

Tsugune-bata-kare-ba: Jam'iyyar PDP na shirin sake darewa gida 2

Mai magana da yawun babbar jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) a mataki na kasa baki daya mai suna Yarima Dayo Adeyeye yayi zargin cewa akwai makarkashiyar da wasu jiga-jigan jam'iiyar ke shiryawa na yin taron gangamin su na daban a ranar 9 ga watan Disemba mai kamawa.

Duk da dai ya zuwa yanzu bai bayyana sunan jiga-jigan ba, amma Yarima Adeyeye ya bayyana cewa suna kokarin yin hakan ne da nufin cusa rudani tare da neman raba kan jam'iyyar bayan rikicin da ta sha a watannin baya.

Tsugune-bata-kare-ba: Jam'iyyar PDP na shirin sake darewa gida 2

Tsugune-bata-kare-ba: Jam'iyyar PDP na shirin sake darewa gida 2

KU KARANTA: Buhari zai sake maido da shingayen karbar haraji

Legit.ng dai ta samu cewa mai magana da yawun jam'iyyar ta APC yayi wannan ikirarin ne a yayin da yake jawabi lokacin taron manema labaran da ya kira a babbar hedikwatar jam'iyyar ta PDP ta Wadata Plaza a garin Abuja.

Haka nan kuma Yarima Adeyeye ya kara kwarmata cewa tabbas wadanda ke shirin yin hakan jam'iyyar dake mulki ta APC ce suke yi wa aiki kuma ba za su samu nasara ba.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel