Kungiyar CAN da na Muslim Council sunyi tir da harin Mubi

Kungiyar CAN da na Muslim Council sunyi tir da harin Mubi

- Kungiyoyin addinan musulunci da na Kirista sun bayyana takaicin su kan hare-hare da aka kai a garuruwan Numan da Mubi

- Kungiyoyin sunyi kira da hukumomin da abin ya rataya kansu su dage wajen binciko wanda suke da hannu a kai hare-haren

- Daga karshe sun shawarci al'umma su cigaba da sa ido da lura da abubuwan da ke faruwa domin rage afkuwar irin wannan abun

Kungiyar Kirista na Najeriya CAN da kuma Kungiyar Muslim Council sunyi tir da wadanda suka kai harin kunan bakin wake a Masallacin Mubi da kuma harin da aka kai a garin Numan wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane da dama.

Shugabanin kungiyoyin Rabaran Stephen Hamza da Alhaji Abubakar Sahabo kuma sunyi kira da wanda abin ya rataya a kan su, su zakulo wadanda suka aika wannan abin takaicin domin su fuskanci hukunci a wani taron manema labarai da suka kira.

Kungiyar CAN da na Muslim Council sunyi tir da harin Mubi

Kungiyar CAN da na Muslim Council sunyi tir da harin Mubi

Hakazalika, Kungiyoyin sun shawarci al'umma su zama masu sa ido da lura da mutane da suke hulda dasu da kuma duba abubuwan hawa kafin su shiga wuraren ibada domin rage afkuwar hare-haren.

DUBA WANNAN: Bidiyo: Sheikh Kabiru Gombe da Sheikh Abdullahi Bala Lau sun tattauna da yan jarida a Landan

Kungiyogin kuma sun kara jadada manufar su ta gina al'umma kan tafarkin zaman lafiya da kaunar juna a duk inda suka sami kansu.

A bayanin da yayi, Sahabo yayi kira da gwamnati ta biya diyya ga iyalan wanda suka rasa rayyukan su kuma ta dauki nauyin mutanen da ke jinya a asibitoci.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ta ruwaito cewa ana kyautata zaton harin da aka kai a garin Numan ranar Litinin da kuma fashewar bam na ranar Talata ayyukan kungiyar yan ta'adda na Boko Haram ne.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel