Nigerian news All categories All tags
Ku shigo APC, ku samu mukamai a Gwamnatin Tarayya, Oshiomhole ya fadawa al'ummar Isoko

Ku shigo APC, ku samu mukamai a Gwamnatin Tarayya, Oshiomhole ya fadawa al'ummar Isoko

- Adams Oshiomhole ya yi kira ga mutanen Isoko da su shiga jam'iyyar APC

- Ya ce yin hakan zai basu damar samun mukamai a Gwamnatin Tarayya

- Ya yi wannan kira ne a walimar karrama tsohon gwamnan Jihar Delta, James Ibori

Adams Oshiomhole a yayin walimar karrama tsohon Gwamnan Jihar Delta, James Ibori, ya ce da mutanen Isoko na Jihar, da su shigo APC don samun mukamai a Gwamnatin Tarayya.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewan a taron wanda ya samu halartar manyan mutane ciki har da Gwamnan Jihar, Oshiomole ya yi kira ga mutanen Isoko da su shiga cikin jam'iyya mai mulki, wato APC, don samun gwababen mukamai a cikin Gwamnatin Tarayya.

Ku shigo APC, ku samu mukamai a Gwamnatin Tarayya, Oshiomhole ya fadawa al'ummar Isoko

Ku shigo APC, ku samu mukamai a Gwamnatin Tarayya, Oshiomhole ya fadawa al'ummar Isoko

Gwamnan Jihar, Ifeanyi Okowa, ya yaba da wannan walimar. Ya kuma yi kira ga al'ummar jihar ta su da su hada kawunan su don cigabar su.

DUBA WANNAN: Tirkashi! Har yanzu akwai al'ummomin da ke riko da al'adan kashe tagwaye a Abuja

Shi kuma Ibori a na sa jawabin, ya yi fatan tabbatuwa da cigabar dimokoradiyayya. Ya kuma mika godiyar sa game da shirya walimar da a ka yi don karrama sa.

Legit.ng ta ruwaito maku yadda Ibori ya fito ya caccaki masu juyayin rashin tsohon Mataimakin Shugaban kasa, Alex Ekwueme. A inda Ibori ya kira juyayin na su a matsayin ihu bayan hari.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel