Nigerian news All categories All tags
Tirkashi! Har yanzu akwai al'ummomin da ke riko da al'adan kashe tagwaye a Abuja

Tirkashi! Har yanzu akwai al'ummomin da ke riko da al'adan kashe tagwaye a Abuja

- NAN ta gano cewan har yanzun akwai mutanen da su ke kashe tagwayen da a ka haifa masu

- Wadannan mutane su na zaune ne yankuna daban-daban na garin Abuja

- Su na aikata wannan danyen aiki ne bisa fahimtar tagwayen za su jawo masu mummunar kaddara

Binciken Hukumar Dillancin Labarai na Najeriya (NAN), ya gano cewan har yanzun wasu al'ummomin garin Abuja ba su daina kashe tagwaye da duk wasu jarirai fiye da guda 1, da jarirai masu wata illa da a ka haifa masu. Su na da fahimtar cewa irin wadannan jarirai, za su janyo masu mummunar kaddara.

Wadannan al'ummomi sun hada da: Gbajingala na Basa Komo, Chukuku, Gaube, Chibiri, Kulo, Kiyi, Gawu, da Sabo, na gundumar Kuje. Sai kuma Dogon Ruwa, Fuka, Gomani, Lapa, Gurugi, Sadaba, Kwala da Keru, na gundumar Kwali. Haka nan kuma su ke kashe kananan yara da su ka fara fitar da hakoran sama kafin na kasa.

Tirkashi! Har yanzu akwai garuruwan da ke riko da al'adan kashe tagwaye a Abuja

Tirkashi! Har yanzu akwai garuruwan da ke riko da al'adan kashe tagwaye a Abuja

NAN ta gano cewan wasu a boye su ke yi wasu kuwa fili su ke yi. Sai dai kuma jin ta bakin al'ummar ya faskara saboda tsoron ka da a bayyana su. Face wani mutum daya tal, mai suna Zaka Musa wanda ke zaune a Kiyi da ya ce masu aikata hakan su na yi ne ba tare da sanin shuwagabannin al'ummomin ba.

DUBA WANNAN: An gurfananar da dan kasuwa a Kebbi bisa safaran sukari mara inganci

Mista Musa ya kuma ce su ne wadanda har yanzun ba su waye ba. Wasu daga cikin shuwagabannin al'ummomin kuwa sun musanta faruwan hakan, a inda wasu kuma su ka tabbatar da faruwar sa a baya. Sai dai sun ce tuni a ka daina yi.

Shi kuwa wani Mishau mai suna Mista Stephen, wanda ya gina gidan marayu a Kuje, ya tabbatar da faruwan hakan. Idan ba'a manta ba dai kisan tagwaye al'ada ce ta mutanen Calabar gabanin wata Mishau mai suna Mary Slessor ta yi hanin hakan, bisa fahimtar daya daga cikin tagwayen shedani ne.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel