Ba gudu ba ja da baya akan hukumomin DSS da NIA - Magu

Ba gudu ba ja da baya akan hukumomin DSS da NIA - Magu

Shugaban hukumar EFCC Ibrahim Magu ya bayyana cewa, har yanzu bai samu wata karaya ba dangane da rashin sa'ar kama tsohon shugaban hukumar DSS (Department of State Security), Ita Ekpeyong da kuma tsohon shugaban hukumar leken asiri ta NIA (National Intelligence Agency), Ayo Oke a ranar Talatar da ta gabata.

Magu ya bayyana hakan a ranar Larabar da ta gabata, yayin ganawa da manema labarai bayan ya halarci taron shugaban kasa Muhammadu Buhari na kafa kwamitin kididdiga akan kudaden da kasar nan ta karbo daga hannayen barayin gwamnati a fadar ta shugaban kasa dake birnin tarayya.

Shugaban hukumar ta EFCC ya jaddada cewa, babu wanda doka ba ta kan shi, kuma hukumar ta na da cikakkun dalilai da shaidu akan tsofaffin shugabannin DSS da NIA.

Legit.ng ta ruwaito tun a ranar Larabar da ta gabata cewa, hukumar EFCC tana zrgin wadannan tsofaffin shugabanni biyu da almundahana ta kudin kasa, inda hukumar EFCC ta aika musu da goron gayyata tun makonni uku da suka gabata amma ba su amsa wannan kira ba.

Shugaban Hukumar EFCC Ibrahim Magu

Shugaban Hukumar EFCC Ibrahim Magu

Hukumar EFCC ta tura ma'aikatan akan su kamo wannan mutanen biyun, inda makarrabansu na tsofaffin ma'aikatun su suka kekashe akan baza su yarda a kama su ba, wanda hakan ya janyo cecekuce a farfajiyar majalisar dattawa.

KARANTA KUMA: Sai Buhari ya yi taka-tsan-tsan akan shugabancin Najeriya - Inji wata Sanata

Hukumar EFCC ta na bincikar Ekpeyong akan laifuka da suke da alaka da harkalar kudin makamai da suka salwanta, wanda tuni babban muhaddasin laifin Kanal Sambo Dasuki da wasu jiga-jigai sun shiga hannu.

Shi kuwa Oke, hukumar ta EFCC tana bincikar akan kudi na Naira Biliyan 13 da aka boye a jihar Legas, wanda tuni hakan ya sanya shugaba Buhari ya sallame shi daga aiki.

LATSA WANNAN: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel