An kama mallamai guda 3 da sassan jikin mutane a Oyo

An kama mallamai guda 3 da sassan jikin mutane a Oyo

- Yansanda sun kama mallaman addini da kafafu da kawunan mutane a Oyo

- Masu laifin sun sato sassan jikin mutane biyu a makabarta musulmai dake Ogbomosho

- Mallaman

Jami’an yansandar jihar Oyo sun kama mallaman addinin musulunci guda 3 da kawuna da kafafu mutane a Oyo dan yin asiri.

Kwamishinan yansadar jihar Oyo Abiodun Odude yace rundunar yansadar SARS su ka kama masu laifin Babatunde Kareem mai shekaru, 37, Taofeek Bello, 22 da Adebayo Yusuf 40 a ranar 14 ga watan Nawumba na shekara 2017 a Ogbomosho.

An kama mallamai guda 3 da sassan jikin mutane a oyo

An kama mallamai guda 3 da sassan jikin mutane a oyo

Odude ya ce masu laifin sun sato kafafuwa da kawunan mutane biyu a makabartar musulmai dake Isale General Area, Ogbomosho.

KU KARANTA : Jam'iyyun APC da PDP sun yi na'am da tsayawa takarar shugaba Buhari a zaben 2019 - Rochas Okorocha

Daya daga cikin masu laifin Taofeek Bello yace su uku mallaman addinin musulunci ne, kuma sana’ar su shine taimakawa mutane da magunguna dan shawo kan matsalolin da suke fuskanta a rayuwar su.

Yansanda sun ce za a kai masu laifin kotu idan sun kammala binciken su.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel