Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi

- Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yi alkawarin tallafa wa hukumar FRSC

- Ganduje ya ce gwamnatinsa ta gudanar da ayyukan gyare-gyaren hanyoyi da dama a jihar

- Shugaban FRSC ya ce yawan gudu da mota ita ne babban abin da yafi kisa a hanyoyi

Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yi alkawarin tallafa wa hukumar tabbatar da tsaron hanyar mota (FRSC), don rage hatsarori sakamakon yawan haɗarin da ake samu a hanyoyi.

Ganduje ya yi wannan alkawarin ne a ranar Laraba, 22 ga watan Nuwamba a lokacin kaddamar da wani shirin wayar da kai mutane wanda hukumar FRSC ta shirya a Kano.

Kamar yadda Legit.ng ke da labari, kwamishinan ayyuka, gidaje da sufuri, Alhaji Aminu Wudil ya wakilci gwamna a taron.

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi

Abdullahi Ganduje na jihar Kano

Ya ce, gwamnatinsa ta gudanar da ayyukan gyare-gyaren hanyoyi da dama don samar da hanyoyi masu kyau a jihar.

KU KARANTA: Sai Buhari ya yi taka-tsan-tsan akan shugabancin Najeriya - Inji wata Sanata

Da yake jawabi a baya, shugaban hukumar ta shiyar arewa maso yamma, Mista Paul Darwang, ya gargadi direbobi kan yawan guje-guje.

"Yawan gudu da mota ita ne babban abin da yafi kisa a hanyoyinmu yanzu haka kamar yadda direbobi ke rasa ikon motar su a lokacin da lamarin ya faru", in ji shi.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel